Fasto ya yi Magana a kan Abin da ya Kai su wajen Kaddamar da ‘Dan takaran APC
Bishof Igbokwe Prince yana cikin Fastocin da suka halarci bikin kaddamar da Kashim Shettima
Faston shi ne babban limamin majami’ar Yoke Breaker Prophetic Ministry da ke ibada a Abuja
Igbokwe Prince ya ce ba su so APC ta tsaida Musulmi ba, amma an yi hakan ne saboda cin zabe
Abuja - Wani daga cikin malaman addinin kiristan da aka gani wajen bikin kaddamar da ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa a APC, ya yi magana.
A wani bidiyo da aka fitar a dandalin sada zumunta na zamani, Igbokwe Prince, ya yi karin haske a kan dalilin wasu Fastoci na zuwa wajen taron da aka yi.
Igbokwe Prince wanda babban Fasto ne a cocin Yoke Breaker Prophetic Ministry na Abuja yake cewa su na girmama matsayar da jam’iyyar APC ta dauka.
Gabatar da Shettima: Kungiyar Kiristoci ta kalubalanci Tinubu da ya bayyana sunayen fastocin da suka je taron
Jam’iyyar APC ta tsaida Musulmi da Musulmi ne a takarar shugaban kasa, hakan ta sa kungiyar kiristoci na kasa watau CAN, ta yi Allah-wadai da tafiyar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Fastoci sun sabawa CAN
Amma Bishof Igbokwe Prince da wasu abokan aikinsa fastoci, sun samu amsa goron gayattan jam’iyyar APC na kaddamar da Sanata Kashim Shettima.
Bishof Prince yake cewa mafi yawansu sun so a ce Yakubu Pam APC ta dauko a matsayin ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Premium Times ta ce Yakubu Pam shi ne shugaban hukumar sauke farali ta kiristocin Najeriya wanda kngiyoyin kiritsoci suka marawa baya.
Duk da ba su samu yadda suke so ba, Faston ya yi kira ga Kiristoci su hakura da wanda APC ta tsaida, domin an yi hakan ne saboda a iya lashe zabe.
Kamar yadda aka ji a bidiyon, Faston ya ce sam bai kamata a rika cakuda harkar addini da siyasa ba.
Jawabin Bishof Igbokwe Prince
"Kungiyoyin kiristoci ba jam’iyyun siyasa ba ne. Abin da jam’iyyar (APC) ta yi, saboda cigaban ta ne, jam’iyyar ta na so ta lashe zabe ne.”
“Mun yi bore sau da yawa, mun goyi bayan kirista ne, Rabaren Yakubu Pam, Shugaban hukumar kula da sauke faralin kiristoci na kasa.”
“Shi mu ka so a dauka a matsayin abokin takarar shugaban kasa, APC tayi abin da zai ta ci zabe ne.”
“Idan ku ka kawo addini a cikin jam’iyyar siyasa, ba za a wanye lafiya ba – Hakan ba zai ba su damar samun nasara a zabe ba.”
NNPP ta na makoki
Kun samu labari wani mummunan hadari ya rutsa da motar ‘Yan Jam’iyyar NNPP a titin Suleja-Lambata, inda aka rasa Shugabannin Jam’iyyar na jihar Neja.
Nan take shugabannin NNPP na Aagie da Kacha suka rasu, sannan wasu jagrorin jam’iyyar na yankin Gbako, Edati, da Lapai suna kwance a asibiti a yanzu.
Asali: Legit.ng