Shirin 2023: Buhari ya shiga wata ganawa da manyan jiga-jigan jam'iyyar APC
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawa da jiga-jigan APC a fadarsa da ke babban birnin tarayya Abuja
- Kwanan nan dan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu ya kaddamar Shettima a matsayin abokin gami na zaben 2023
- Jam'iyyun siyasa a Najeriya na ci gaba da shirin tunkarar zaben 2023 mai zuwa watanni kadan masu zuwa
FCT, Abuja - A halin yanzu dai shugaban kasa Muhammadu Buhari na can na ganawa da wata tawaga ta jiga-jigan jam'iyyar APC a fadar shugaban kasa da ke Abuja, rahoton Punch.
Tawagar wacce ta kunshi shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, mataimakin kakakin majalisar wakilai, Idris Wase, Kashim Shettima, da sauran manyan ‘ya’yan jam’iyyar, ya zo ne domin ganawa da Buhari da misalin karfe 03:00 na yamma a yau Juma'a.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon kakakin majalisar wakilai, Dimeji Bankole, tsohon ministan noma, Audu Ogbe da tsohon babban hafsan sojin sama Air Marshall Sadiq Abubakar.
Sauran jiga-jigan APC da suka halarci ganawar
Haka kuma akwai wasu mambobin kungiyar gwamnonin APC da suka hada da Babagana Zulum na Borno, Inuwa Yahaya na Gombe, Abdullahi Sule na Nasarawa da Abubakar Bagudu na Kebbi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, da Sanata mai wakiltar Taraba ta kudu, Emmanuel Bwacha, su suma sun halarci taron.
Sai dai ba a ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ba, Bola Tinubu har lokacin hada wannan rahoton.
Ziyarar ta zo ne kwanaki biyu kacal bayan kaddamar da Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu a zaben 2023 mai zuwa.
Wasu hotuna da hadimin Buhari kan harkokin yada labarai ya fitar sun nuna shugaban da jiga-jigan na APC.
Gwamnatin Buhari za ta kashe N6.72trn a matsayin tallafin man fetur a 2023
A wani labarin, gwamnatin tarayya ta ce za ta tanadi kudaden tallafin man fetur a shekarar 2023 da akalla za su kai sama da Naira tiriliyan 6.72.
Ministar Kudi ta Kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan a Abuja ranar Alhamis yayin taron kashe kudade na 2023 – 2025 na MTEF da FSP, The Nation ta ruwaito.
Zainab Ahmed ta ce gwamnati ta yi hasashen sakamakon kasafin kudi matsakaici ta fuska da yanayi biyu dangane da ma'auni na kasafin kudin Najeriya.
Asali: Legit.ng