Atiku Abubakar: Ban Taba Zama Fiye Da Wata Daya a Dubai Ba
- Dan Takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya ce bai taba zama fiye da wata daya a lokaci guda ba a Dubai
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ranar Juma'a
- Atiku ya ce lokacin kawai da ya dade a Dubai shine lokacin da ya yi karatun digirinsa na biyu (Masters), yana mai cewa kafafen watsa labarai da abokan hammayarsa ne ke zuzuta abin
Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya ce bai taba zama fiye da wata guda ba a Dubai bayan lokacin da ya yi karatun digirinsa na biyu, Nigerian Tribune ta rahoto.
Tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya ya bayyana hakan ne a yayin hira da aka yi da shi a Arise TV a ranar Juma'a.
Mai fatan zama shugaban kasar ya ce:
"Babu wani naci da na ke yi wa Dubai. Abu ne kawai na kafafen watsa labarai suka kitsa. Eh, Na tafi Dubai na dan wani lokaci kuma na yi amfani da lokacin na yi digiri na biyu. Wannan shine lokaci mafi tsawo da na yi a Dubai.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Bayan haka, ban taba zama fiye da wata guda daya a lokaci guda ba a Dubai. Don haka abu ne kawai da kafafen watsa labarai suka kwallafa ido a kai ko kirkira. Abokan hamayya da dama suna ta magana kan Dubai da sauransu su."
Atiku: Tikitin Musulmi Da Musulmi Yasa Ban Amince Da Tinubu Ba Lokacin Da Yake Son Zama Abokin Takara Na
A wani rahoton daban, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce kauracewa tikitin musulmi da musulmi yasa ya ki yarda Asiwaju Bola Tinubu ya yi masa mataimaki a zaben shekarar 2007, The Cable ta rahoto.
Atiku, wanda ya yi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo mataki daga 1999 zuwa 2007, ne ya bayyana haka yayin wata hira da aka yi da shi a ARISE TV a ranar Juma'a.
Atiku ya samu matsala da Obasanjo a yunkurinsa gadon kujerarsa, amma daga baya ya samu tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Action Congress, AC, jam'iyyar da Tinubu ya taimaka wurin kafa ta bayan 'guguwar' siyasa ta tarwatsa gwamnonin AD da aka zaba a 1999.
Asali: Legit.ng