Yanzu Yanzu: Tinubu ya magantu a kan manyan Bishop-Bishop da aka gani a wajen gabatar da Shettima

Yanzu Yanzu: Tinubu ya magantu a kan manyan Bishop-Bishop da aka gani a wajen gabatar da Shettima

  • Kungiyar yakin neman zaben Tinubu ta yi martani ga zargin cewa malaman addini da aka gano a wajen gabatar da Shettima duk na bogi ne
  • Daraktan yada muradu na kungiyar TCO, Bayo Onanuga, ya ce malaman da suka halarci taron APC ba na bogi bane kuma shugabannin coci ne na hakika
  • Onanuga ya ce koda dai malaman basu yi suna ba a daular Kiristanci, suna nan suna gina muradansu a hankali

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya mayar da martani ga masu suka, wadanda suka zargi tawagarsa da yin hayar masu yawo a titi da kuma shirya su a matsayin malaman Kirista a wajen gabatar da abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima a Abuja.

Kara karanta wannan

Dan takarar APC Tinubu: Dole ne na kwaci Najeriya a 2023 don na samar da ayyukan yi

A cikin wata sanarwa ta hannun kungiyar yakin neman zabensa, Tinubu ya ce an bude taron ne ga kowa, ciki harda malaman addini, jaridar Vanguard ta rahoto.

Malaman Kirista
Yanzu Yanzu: Tinubu ya magantu a kan manyan Fastocin da aka gani a wajen gabatar da Shettima Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Daraktan yada muradu na kungiyar ta TCO, Bayo Onanuga ya zargi yan adawa da shiga lamarin don kai hare-hare mara amfani kan APC.

Onanuga ya kuma bayyana yayata hotuna da bidiyoyin wasu malamai maza da mata da suka halarci taron da ake tayi a matsayin ‘kokarin janye hankali mara dalilili’.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Onanuga ya ce:

“Taro ne na wani lamari da yake a bude, wanda ya baiwa jama’a damar halarta, ciki harda malaman addini da sauransu wanda a yanzu karen farautar yan adawa ke yi masu ba’a."

Ya kuma jadadda cewa wadannan malamai da aka gani ba na bogi bane, ba kanikawa bane ko masu siyar da doya kamar yadda magauta ke kokarin cusa hakan a zukatan yan Najeriya a shafukan soshiyal midiya, rahoton The Sun.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Wani shugaban APC ya yi ta maza, ya tsere daga hannun 'yan bindiga

Ya kara da cewa:

“Su ba manya bane tukunna a addinin Kiristanci, suna gina muradansu ne a hankali.
“Su shugabannin coci ne wadanda suka yarda cewa dole yan Najeriya su nisanci siyasar kiyayya da na addini sannan a maimakon haka su rungumi siyasar zaman lafiya da gina kasa.”

Daga karshe ya bayyana cewa kamfen dinsu ya karkata ne a kan manyan lamuran da ke damun gwamnati wanda ya shafi dukka yan Najeriya da nufin magance su da kuma kawo ci gaba a rayuwar mutanen kasar.

Kungiyar CAN Ta Nesanta Kanta Da Bishop-Bishop Da Suka Hallarci Kaddamar Da Shettima

A baya mun ji cewa kungiyar Kiristocin Najeriya CAN, a ranar Laraba ta nesanta kanta daga Bishop-Bishop da suka hallarci kaddamar da dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, Kashim Shettima, suna cewa don wata manufar kashin kansu suka tafi.

Kungiyar ta ce duk da cewa dan takarar shugaban kasar na APC, Bola Ahmed Tinubu, yana da ikon "daukar hayar makanikai da wasu masu sana'ar hannu ya dinka musu riguna amma hakan ba zai canja bukatar da ke akwai na yin adalci ba."

Kara karanta wannan

2023: Ba don ra'ayin kaina na zabi Shettima ba, Tinubu ya fadi dalilin zabo mataimakinsa

Mataimakin shugaban CAN na (Jihohi 19 da Abuja) da shugabanta a Kaduna, Rabaran Jospeh Hayab ne ya furta hakan a wani hira da yayi da manema labarai a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng