Dan takarar APC Tinubu: Dole ne na kwaci Najeriya a 2023 don na samar da ayyukan yi

Dan takarar APC Tinubu: Dole ne na kwaci Najeriya a 2023 don na samar da ayyukan yi

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya bayyana dalilin da yasa yake son gaje Buhari, kuma dole ne ya ci zabe
  • Tinubu ya sha fadi cewa, zai kawo sauyi Najeriya ta hanyar dabbaka abubuwan da ya cimma a lokacin da yake gwamnan Legas
  • An sha cece-kuce lokacin da Tinubu ya bayyana Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a zaben 2023 mai zuwa

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya bayyana kadan daga tagomashin da ya tanadarwa 'yan Najeriya, inda ya dage cewa dole ne ya ci zabe.

Bola Ahmad Tinubu, ya magantu ne yayin da yake kaddamar da abokin takararsa Kashim Shettima a babban birnin tarayya Abuja.

Tinubu, ya bayyana cewa, yana da mafarkin kawo sauyi a Najeriya, kuma zai tabbatar da samar da ayyukan yi ga 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Ba don ra'ayin kaina na zabi Shettima ba, Tinubu ya fadi dalilin zabo mataimakinsa

Tinubu ya ce dole ya karbi Najeriya domin kawo sauyi cikin gaggawa
Dan takarar APC Tinubu: Dole ne na ci zaben nan domin na samar da ayyukan yi | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A bangare guda, ya kuma ce zai tabbatar da an samu ilimi mai inganci, a tarbiyyantar da kananan yara son kasa da kaunar zaman lafiya da hakuri da juna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kafar yada labarai ta Channels ta naqalto Tinubu na cewa:

“Dole ne mu ci wannan zaben domin mu kawo ayyukan yi, mu kawar da talauci, mu tarbiyyantar da ‘ya’yanmu, mu tarbiyyantar da jikokinmu ba tare da tunanin rarrabuwar kawuna ko kabilanci ba, duk daya muke, fasfo dinmu daya ne, koren takinmu daya ne, kasa daya. Makoma daya."

Cece-kuce bisa zabo Shettima a matsayin abokin takara

Makwanni kadan ne dan takarar shugaban kasa a APC, Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana Kashim Shettima a matsayin wanda zai tsaya masa a zaben 2023.

Sai dai, wannan zabe ya jawo cece-kuce da martani daga bangarori da dama a kasar nan, ciki har da kungiyoyin addini.

Kara karanta wannan

2023: APC, PDP Na Fuskantar Babban Barazana A Yayin Da Peter Obi Ya Fara Kamfen A Arewa, Ya Ziyarci Dattijon Arewa Mai Karfin Fada A Ji

Kungiya ta gaba da ta nuna damuwa kan wannan zabe ita ce CAN, inda ya bayyana cewa, akwai yiwuwar kiristan Najeriya su fada wani hali.

2023: Ba don ra'ayin kaina na zabi Shettima ba, Tinubu ya fadi dalilin zabo mataimakinsa

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi bayanin cewa ya zabi abokin takara daga cikin yan arewa marasa rinjaye ne saboda ci gaban kasar gabaki daya.

Tinubu ya bayyana hakan ne gabannin bayyana Alhaji Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a hukumance a ranar Laraba a Abuja, jaridar Independent ta rahoto.

Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya ce da ace yana tunanin samun tarin kuri’u ta hanyar amfani da kabilanci ne toh zai zabi mataimaki daga yankin arewa maso yamma ne domin a cewarsa ita ce ta fi yawan masu rijistan zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.