Gudaji Kazaure: Na sauya sheka daga APC zuwa ADC, amma har gobe ni dan kashenin Buhari ne

Gudaji Kazaure: Na sauya sheka daga APC zuwa ADC, amma har gobe ni dan kashenin Buhari ne

  • Hon. Muhammad Gudaji Kazaure ya jadadda cewar har gobe shi dan kashenin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne
  • Dan majalisa mai wakiltan mazabar Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi a majalisar kasa ya ce ya sauya sheka daga APC zuwa ADC don samun damar komawa kan kujerarsa
  • Kazaure ya zargi Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa da hana masa tikitin APC ba tare da wani kwakkwaran dalili ba

Jigawa - Dan majalisar wakilai ta kasa daga jihar Jigawa, Muhammad Gudaji Kazaure, ya bayyana cewa ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa African Democratic Congress (ADC).

Sai dai kuma, Kazaure ya ce har yanzu yana nan a matsayinsa na dan kashenin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, jaridar The Cable ta rahoto.

Gudaji Kazaure tare da Buhari
Gudaji Kazaure: Na sauya sheka daga APC zuwa ADC, amma har gobe ni dan kashenin Buhari ne Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa a ranar Talata, 19 ga watan Yuli, Kazaure ya ce gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru, ya hana masa tikitin komawa majalisar haka siddan, babu gaira ba dalili.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Zullum ya maye gurbin Shettima a matsayin dan takarar APC a Borno ta tsakiya

A yayin zaben fidda gwanin APC, dan majalisar ya rasa tikitin jam’iyyar inda Muktar Zanna, Shugaban karamar hukumar Kazaure ya yi nasara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zanna ya lashe tikitin jam’iyyar mai mulki bayan ya samu kuri’u 89.

Muhammad Zakari, wanda shima ya nemi takarar tikitin ya samu kuri’u 70, yayin da Kazaure ya zo na uku da kuri’u 26.

Dan majalisar wanda ke wakiltan mazabar Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi a majalisar, ya ce yana da yakinin lashe zabe a karkashin jam’iyyar ADC.

Jaridar ta nakalto Kazaure yana cewa:

“Eh na bar jam’iyyar APC, amma biyayyata ga shugabanmu, Muhammadu Buhari da al’ummar Najeriya na nan daram dam.
“Gwamna na ya hana ni tikitin komawa majalisa babu gaira babu dalili amma hakan bai canja komai ba, na koma ADC kuma mutanena sun bani tabbacin nasara.”

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Allah ya yiwa dan majalisa, Olusegun Popoola, rasuwa

Dan majalisar wanda aka fara zaba a 2015, ya kasance rikakken dan kashenin shugaban kasa.

2023: Sabon sabani ya kunno kai a APC kan wanda Tinubu ya zaba mataimaki, Gwamna El-Rufa'i ya fusata

A wani labari na daban, mun ji cewa Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna bai ji dadin hukuncin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya yanke ba na zabar tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa.

Jaridar Daily Independent ta rahoto daga wasu majiyoyi cewa shugabancin APC na kokarin ganin ta sasanta lamarin a cikin gida ta yadda ba zai fita waje kamar na jam’iyyar PDP da gwamnan jijar Ribas, Nyesom Wike ba.

Kamar yadda yake a yanzu, alaka ta yi tsami tsakanin Wike da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar wanda ya sanar da Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takararsa.

Kara karanta wannan

2023: Na sanyawa Tinubu da Shettima albarka, in ji Ali Modu Sheriff

Asali: Legit.ng

Online view pixel