Musulmi Ke Da Kashi 65 cikin 100 A Yankin Kudu Maso Yamma, In Ji Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu

Musulmi Ke Da Kashi 65 cikin 100 A Yankin Kudu Maso Yamma, In Ji Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu

  • Adebayo Shittu, tsohon Ministan Sadarwa kuma shugaban kungiyar yakin neman zaben Tinubu a 2023 ya ce musulmi sune ke da kashi 65 cikin 100 na mutanen kudu maso yamma
  • Shittu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a lokacin da ya ke kare zabin da mai gidansa ya yi na daukan mataimaki musulmi kuma daga arewa
  • Shugaban kungiyar kamfen din ya kuma bada misalai na jihohi da suka hada da Ekiti, Edo da Ondo inda aka yi tikitin kirista da kirista amma mutane ba su tada hayaniya ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Direkta Janar na Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu, Adebayo Shittu, ya yi ikirarin cewa musulmi ne ke da kashi 65 cikin 100 na al'ummar kudancin Najeriya.

Ya yi wannan furucin ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na AIT, a shirin Focus Nigeria, ranar Talata, Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya sace janareto da lasifikar Masallaci a Adamawa, ya sheke kudin a tabar wiwi

Adebayo Shittu
Musulmi Ne Ke Da Rinjaye A Yankin Kudu Maso Yamma, In Ji Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben Tinubu. Hoto: @PremiumTimesNg.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shittu yana bada hujja ne kan batun daukan mataimaki musulmi, wato Kashim Shettima da Tinubun ya yi gabanin zaben 2023.

Kungiyar CAN da wasu yan jam'iyyar APC da masu ruwa da tsaki sun ta babatu kan tikitin musulmi da musulmin da Tinubu ya yi.

Da ya ke nuna cewa abin da mai gidansa ya yi ba laifi bane, Shittu ya ce galibin mutanen yankin kudu maso yamma musulmai ne.

"A kudu maso yammacin Najeriya, musulmi sune ke da kashi 65 cikin 100," na al'umma in ji lauyan.
Da aka masa tambaya idan abin da ya fada hasashe ne ko kuma daga alkalluma ta kididdiga ne, ya ce, "Ba na karya. Kana iya zuwa ka yi duba. Ka yi binciken ka," in ji shi.
Ya kara da cewa, "A kan addini ne mutane suke ta maganganu kan tikitin musulmi da musulmi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Babu Gudu Babu Ja Da Baya' ASUU Ta Dora Wa Ministan Kwadago Laifin Tsawaita Yajin Aiki

"A Ekiti, an yi tikitin kirista da kirista. A Ondo, kirista da kirista. A Edo, inda arewacin jihar mafi yawanci musulmi ne, nan ma tikitin kirista da kirista aka yi. Babu wanda ke surutu kan hakan."

A baya bayan nan, batun ya dauki hankulan sassan mutane da dama har ta kai ga kungiyar Kirista ta Najeriya CAN ta shawarci mambobinta su guji zaben duk jam'iyyar da tsayar da masu addinai daya a zaben shugaban kasa.

Tsoron Tinubu Da Shettima Yasa Yan Adawa Ke Babatu Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi, Kungiya

A bangare guda, Mallam Abdulazeez Yinka Oniyagi, Jagoran Kungiyar Goyon Bayan Tinubu (TSO) ya ce tsoron Tinubu da Shettima ne yasa masu adawa ke daukan nauyin masu dumama siyasa kan batun tikitin musulmi da musulmi.

Hakan ne zuwa ne a lokacin da Direkta Janar na TSO, Hon Aminu Suleiman ya ce kungiyar za ta koma ta yi nazari don kaucewa 'kuskuren' da jam'iyyar ta yi a Jihar Osun ranar Asabar.

Kara karanta wannan

2023: Ba Za Mu Bari Mambobin Mu Su Zabi Musulmi Da Musulmi Ba, In Ji Matasan Kungiyar CAN

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164