Yanzu-Yanzu: 'Babu Gudu Babu Ja Da Baya' ASUU Ta Dora Wa Ministan Kwadago Laifin Tsawaita Yajin Aiki

Yanzu-Yanzu: 'Babu Gudu Babu Ja Da Baya' ASUU Ta Dora Wa Ministan Kwadago Laifin Tsawaita Yajin Aiki

  • Kungiyar malaman jami'o'i ta Najariya, ASUU, ta ce babu batun janye yajin aikin da ta shafe kusan watanni tana yi har sai an biya mata bukatunta
  • Farfesa Emmanuel Osodeke, shugaban kungiyar ASUU na kasa ne ya bayyana hakan yayin wani jawabi da ya yi wa manema labarai a Abuja a ranar Talata
  • Shugaban na ASUU ya ce Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Dr Chris Ngige ne dalilin da yasa har yanzu tattaunawarsu bata cimma haka ba saboda karerayi da ya ke yi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya, ASUU, ta dage cewa ba za ta janye yajin aikin da mambobinta ke yi ba a kasar, wanda a yanzu suke watansu na biyar.

Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ne ya bayyana hakan a yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a Abuja, rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

2023: Ba Za Mu Bari Mambobin Mu Su Zabi Musulmi Da Musulmi Ba, In Ji Matasan Kungiyar CAN

Mambobin ASUU.
Yanzu-Yanzu: 'Babu Ja Da Baya' ASUU Ta Dora Wa Ministan Kwadago Laifin Tsawaita Yajin Aiki. Hoto: @ChannelsTV.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamai a jami'o'in gwamnati sun fara yajin aikin na duka kasa a ranar 14 ga watan Fabrairu kan tsarin biyan albashi na IPPIS da gwamnati ke amfani da shi wurin biyansu.

Sun kuma koka kan karancin kudade na raya jami'o'i, rashin biyan albashi da allawus din wasu takwarorinsu, a rashin biyan wasu kudade da sauransu.

Tun fara yajin aikin, an yi ta taron tattaunawa tsakanin kungiyar da gwamnati amma ba a cimma matsaya na janye yajin aikin ba.

Kungiyoyi daban daban da daidaikun mutane a kasar sun yi ta kira ga gwamnati ta karo karshen yajin aikin da malaman ke yi.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a Abuja, Farfesa Osedeke ya ce Ministan Kwadago Da Samar Da Ayyuka, Chris Ngige ne ke da laifi kan abin da ke faruwa a yanzu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya fusata, ya fadi ranar da yake so ASUU su janye yajin aiki

Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Talata ya umurci ministan Ilimi, Adamu Adamu da takwarorinsa su kawo karshen yajin aikin da ya ki ci ya ki cinye wa.

Da ya ke magana a Abuja, Osodeke ya ce, "Ba za mu bari ministan ya rika mana sharri ba. Ngige ya cigaba da mana sharri ta hanyar sharara karya.
"Sun dakatar da albashin mu suna tunanin hakan zai saka mu koma aiki. Su zauna kamar yadda shugaban kasa ya umurta."

Shugaban ASUU Ya Ƙi Karbar Tallafin N50m Daga Ahmed Isah Don Janye Yajin Aiki

A wani rahoton, wani abu mai kama da dirama ya faru a lokacin da kungiyar malaman jami'o'i na Najeriya, ASUU ta ki karbar kudin da Berekete Family Radio ta bata don janye yakin aiki, rahoton Daily Trust.

ASUU ta fara yajin aiki ne tun watan Fabrairu kuma kawo yanzu duk wani yunkuri da aka yi na ganin malaman sun koma aji bai yi wu ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda yan Hisbah suka kama wani matashi da ya tara gashi, suka yi masa askin kwalkwabo

A safiyar ranar Asabar, mai gabatar da shirye-shirye a rediyo, Ahmad Isah, da aka fi sani da Ordinary President ya gayyaci shugaban ASUU don yi wa yan Najeriya bayani kan matsalolin da suke fuskanta da dalilin da yasa ba su janye yajin aikin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel