Zaben da za ayi a 2023 sai ya fi kowane kyau a tarihin Najeriya inji Shugaban INEC

Zaben da za ayi a 2023 sai ya fi kowane kyau a tarihin Najeriya inji Shugaban INEC

  • Hukumar zabe mai zaman kan ta, ta yi alkawarin zaben 2023 zai zama mafi kyawun da aka taba yi
  • Shugaban INEC na kasa, Mahmood Yakubu ya yi wannan bayani da ya gana da kungiyoyin IRI da NDI
  • Farfesa Mahmood Yakubu ya ce INEC ta cika alkawarin da ta dauka a zaben jihohin Ekiti da Osun

Abuja - Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi alkawarin zaben 2023 zai zama mafi kyawun zaben da aka taba yi a kasar nan.

Kamar yada INEC News ta rahoto, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi wannan bayani a lokacin da ya gana da wasu wakilai da kungiyar IRI da NDI ta kasa.

Shugaban hukumar zaben mai zaman kan ta ya tabbatar da cewa INEC za ta kara kokari bayan irin nasarar da ta samu wajen gudanar da zaben Osun.

Kara karanta wannan

Matasan Kirista a Najeriya Sun Bukaci INEC Ta Kara Tsawaita Kwanakin Rajistan Zabe

Yadda INEC ta yi alkawari, kuma ta cika a zabukan Ekiti da na Osun, Farfesa Yakubu ya ce babban zaben 2023 da za ayi, zai kasance mafi kyawu a tarihi.

Kyawun alkawari cikawa

“Mu na tabbatar maku da cewa za mu cigaba da kokari ba sosai kurum ba, a sosai na gaske wajen ganin mun gudanar da babban zaben 2023.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“A game da shirye-shiryen zaben na 2023, ina so in tabbatar maku da cewa mun yi alkawarin zaben jihar Ekiti zai yi kyau, kuma ya yi kyawun.”
Shugaban INEC
Jami'an INEC da wakilan IRI da NDI Hoto: @inecnigeria
Asali: Twitter
“Mun yi alkawarin zaben Osun zai fi shi, kuma na Osun ya fi kyawu. Mu na alkawarin cewa zaben 2023 zai fi kowane zabe da aka taba yi kyau.”
“Kuma a shirye mu ke wajen ganin mun gudanar da zaben da ya fi kowane kyau a tarihi.”

Kara karanta wannan

Da na sha kaye a zabe inda Buhari bai rattaba hannu kan dokar zabe ba - Adeleke

Frank LaRose ya yi jawabi

The Guardian ta kawo wannan rahoto, ta ce Sakataren gwamnatin jihar Ohio, Frank LaRose, ya yi jawabi a wajen ganawar su da shugaban hukumar zaben kasa.

LaRose wanda jami’in zabe ne a jihar Ohio ta Amurka, ya yabi zuwansa Najeriya da ya yi a karon farko, ya ce dama ce da INCE za ta inganta harkar zabe a kasar.

Jami’in ya ce sun ganewa kansu zaben gwamnan da aka yi a Osun domin shi ne karo na biyu da ake gudanar da zabe a karkashin sabuwar dokar da aka kawo.

Peter Obi yana ta shiri

A baya an ji labari cewa Peter Obi da abokin takararsa watau Yusuf Datti Baba-Ahmed sun sa labule da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo a Ogun.

Kwanan nan Obi ya ziyarci daya daga cikin Dattawan Arewa, Ango Abdullahi a Zaria. Dama can ana rade-radin Obasanjo ya fara tallata shi a wasu yankin Arewa.

Kara karanta wannan

Shugaban APC: Sam ba na raina abokin hamayya, amma dole mu ci zabe a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng