Peter Obi da Abokin takararsa sun zauna da tsohon Shugaban kasa a kan shirin 2023

Peter Obi da Abokin takararsa sun zauna da tsohon Shugaban kasa a kan shirin 2023

  • Peter Obi ya kai wa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ziyara a gidansa da ke Ogun
  • Dr. Yusuf Datti Baba-Ahmed ya yi wa ‘Dan takaran Shugaban kasar rakiya zuwa garin na Abeokuta
  • Ana rade-radin Olusegun Obasanjo yana cikin masu marawa Obi a zaben shugaban Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ogun - Labari ya zo cewa ‘dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya kai wa Cif Olusegun Obasanjo ziyara har gidansa.

Rahoton da jaridar Vanguard ta fitar, ya bayyana cewa Peter Obi sun sa labule da tsohon shugaban kasar ne a ranar Lahadi. 18 ga watan Yuli, 2022.

Obi ya samu rakiyar abokin takararsa a zaben shugaban kasa, Dr. Yusuf Datti Baba-Ahmed.

Tsohon shugaban na Najeriya ya gana da masu neman shugabancin Najeriyan a 2023 ne a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Peter Obi: : Sowore Ya Bayyana Tsaffin Shugabanin Najeriya 3 Da Jigon Arewa Da Ke Goyon Bayan Jam'iyyar Labour Party

Oseloka Obaze da Ituah Ighodalo sun halarta

Yayin da Obasanjo ya karbi bukuncin ‘yan takaran, an samu labarin cewa fitaccen ‘dan gwagwaramyar nan, Ituah Ighodalo ya na wajen taron.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda mu ka samu labari, Fasto Ighodalo babban Limami ne a cocin Trinity House.

Peter Obi da Abokin takararsa a Ogun
Peter Obi, Yusuf Datti Baba-Ahmed da Olusegun Obasanjo Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Abokin siyasar Peter Obi, Oseloka Obaze wanda tsohon jami’i ne a majalisar dinkin Duniya, ya yada hotunan zaman na su a shafukan sada zumunta.

Oseloka Obaze shi ne ya yi wa jam’iyyar hamayya ta PDP takarar kujerar gwamna a zaben jihar Anambra a 2017, wanda Willie Obiano ya yi nasara.

Daily Post ta ce ana tunanin haduwar Obi, Baba Ahmed da mutanen Obasanjo yana cikin shirye-shiryen ‘yan takarar LP na zabe mai zuwa a 2023.

Biri ya yi kama da mutum

Ziyarar da Peter Obi ya kai wa tsohon shugaban kasar ta na zuwa jim kadan bayan ya ziyarci Farfesa Ango Abdullahi, daya daga cikin manyan Arewa.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Kada ku yarda wani fasto ko limami ya fada maku wanda za ku zaba, Keyamo ga yan Najeriya

Hakan ya kara nuna akwai yiwuwar Obasanjo yana goyon bayan takarar Peter Obi a zaben 2023.

Kwanakin baya aka ji labari Mahadi Shehu yana cewa makasudin zuwa Olusegun Obasanjo jihohin Arewa shi ne tallatawa yankin takarar Peter Obi.

A wata hira da aka yi da shi, 'dan kasuwan ya ce Obasanjo yana tare da Obi a 2023, bai goyon bayan Atiku Abubakar, Bola Tinubu ko Rabiu Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel