Tambuwal, wasu ‘Yan siyasa na fuskantar daurin gidan yari a dalilin saba dokar zabe
- Sabuwar dokar zaben shekarar 2022 ta haramta neman kujera biyu a lokacin zabe daya a Najeriya
- Wanda aka samu ya sabawa wannan doka zai iya samun kan shi a gidan yari har na shekaru biyu
- Jami’in INEC, Mike Igini ya yi fashin baki kan dokar a lokacin da ya yi hira da manema labarai
Abuja - Duk wani ‘dan siyasa da ya saye fam din shiga takara fiye da daya a Najeriya, yana fuskantar barazanar daurin shekaru biyu a gidan gyaran hali.
Babban kwamishinan zabe na jihar Akwa Ibom, Mike Igini ya fadi haka yayin da aka yi hira da shi a shirin hantsi na gidan talabijin Channels a ranar Talata.
Babban jami’in na INEC yake cewa a dokar zabe na shekarar 2022, sashe na 115 (D) ya bukaci a daure duk wanda ya saye fam din shiga takara fiye da daya.
Abin da dokar kasa ta ce
“Duk wanda ya sa hannu a takardar shiga zabe ko takardar sakamako a matsayin ‘dan takara a kujeru biyu a zabe daya (ya saba doka mai hukuncin daurin shekara biyu).”
- Mike Igini
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Igini ya yi karin haske, ya ce takara a dokar zabe na nufin shiga zabe dabam-dabam; kujerar shugaban kasa, gwamna, sanata, majalisar wakilan ko na dokoki.
Duk ‘dan siyasar da aka samu ya aikata wannan laifi, ya sabawa sashe na 115 na sabuwar dokar zabe, kuma an yi tanadin daurin da ba zai wuce shekaru biyu ba.
“Sashe na 115 (3) na dokar zaben kasar cewa ya yi bai halatta ‘dan takara ya yi niyyar sayen fam fiye da daya ba, neman kujeru biyu a lokaci guda kuwa, laifi ne.”
“Baya ga damar cin tarar kudi, sashe na K na dokar ya yanke daurin shekaru biyu a gidan maza.”
- Mike Igini
Rashin sani ba uzuri ba ne - INEC
Igini ya ce wasu ‘yan siyasa sun yi hakan a zaben 2023, su na ikirarin sun jahilci dokar, amma jami’in ya ce jahiltar dokar ba uzuri ba ne a wajen hukumar INEC.
Daily Trust ta ce wadanda dokar za ta iya aiki kan su idan har sun nemi kujeru biyu, sun kunshi Dr. Ahmad Lawan, Aminu Tambuwal da kuma Godswill Akpabio.
A Akwa Ibom ta Arewa maso yamma, Godswill Akpabio yana ikirarin shi ne ‘dan takaran Sanata bayan da farko ya saye fam na neman zama shugaban kasa a APC.
Tambuwal sun saba doka?
Ku na da labari cewa shi ma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya shiga takarar Sanata a PDP a majalisar Dattawa da ya gagara zama ‘dan takaran shugaban kasa.
Irin wannan rikici APC ta kefa ma da shi a Yobe, Bashir Sheriff Machina ya ce shi ya lashe tikitin Sanatan Arewacin jihar, ba Ahmad Lawan da aka bada sunansa ba.
Asali: Legit.ng