Abokin takara: A karshe APC ta sa ranar da Tinubu zai kaddamar da Shettima
- An bada sanarwa cewa a ranar Laraba Asiwaju Bola Tinubu zai kaddamar da Kashim Shettima
- Jam’iyyar APC ta fitar da jawabi ta bakin Suleiman Argungu, ta ce za a gabatar da Shettima ga Duniya
- Tun a lokacin bikin Sallah dai Tinubu ya ce Sanata Kashim Shettima ne zai zama Mataimakin na sa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - ‘Dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya tsaida sabon lokacin da zai gabatar da Kashim Shettima.
Punch ta kawo rahoto a ranar Talata. 19 ga watan Yuli 2022, da ya tabbatar da cewa a gobe Laraba Asiwaju Bola Tinubu zai kaddamar da Kashim Shettima.
Hakan na zuwa ne kwanaki kusan goma da ‘dan takaran na APC ya zabi Sanata Kashim Shettima.
Sanarwar gabatar da ‘dan takarar mataimakin shugaban kasar ya fito ta bakin sakataren gudanarwa na jam’iyya mai mulki watau Suleiman Argungu.
Shettima: Yan Najeriya Sun Tattare Kan Addini Yayin Da Sauran Kasashe Ke Kara Azama a Bangaren Fasaha
Suleiman Argungu ya fitar da jawabi da ya nuna APC da Asiwaju Bola Tinubu za su gabatar da ‘dan takarar mataimakin shugabancin kasan a bainar jama’a.
Ana gayyatar manyan APC
Leadership ta ce ana gayyatar duka shugabannin majalisar zartarwa, gwamnoni, ‘yan majalisa da ‘yan majalisar zartarwa na gwamnatin APC wajen taron.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sauran wadanda Jam’iyyar APC ta aikawa gayyata sun hada da wadanda suka nemi tikitin takarar shugaban kasan 2023 da duka shugabannin APC na jihohi.
Har ila yau, ana sa ran ganin Jakadun Najeriya wajen kaddamar da ‘dan takaran na zaben 2023.
Taron zai gudana a dakin taron cibiyar Shehu Yaradua a birnin tarayya Abuja. Watakila an zabi wurin ne saboda rawar da ‘Yar’adua ya taka a zaben 1993.
Tikitin Musulmi da Musulmi
Sanarwar ta nuna Bola Tinubu ya yi watsi da matsin lamba daga wasu da ke ganin bai yi adalci ba tun da ya ki dauko Kirista a matsayin abokin tafiyarsa a 2023.
Wannan mataki ya tabbatar da cewa Sanatan Borno ta tsakiya, Kashim Shettima shi ne zai rike tutar jam’iyyar mataimakin shugaban kasa a zaben shekarar badi.
Peter Obi sun ziyarci OBJ
Ku na da labari Peter Obi da Abokin takararsa watau Yusuf Datti Baba-Ahmed sun sa labule da tsohon Shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo a jihar Ogun.
Kwanan nan Obi ya ziyarci daya daga cikin Dattawan Arewa, Ango Abdullahi, dama can ana rade-radin Obasanjo ya fara tallata shi a wajen wasu manyan Arewa.
Asali: Legit.ng