Rikicin PDP: Akwai yarinta tattare da Wike, wasu ne suke zugo shi inji Sule Lamido

Rikicin PDP: Akwai yarinta tattare da Wike, wasu ne suke zugo shi inji Sule Lamido

  • Sule Lamido ya yi watsi da surutan da wasu ke yi saboda ‘dansa ya samu takarar Gwamna a PDP
  • Tsohon gwamnan jihar Jigawan ya yi kira ga Nyesom Wike ya dauki darasi da irinsu Peter Odili
  • Wike ya nemi takaran PDP a zaben 2023, amma bai dace ba, Sule ya ce ba kan shi ne farau ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi wata hira ta musamman da BBC Hausa, inda ya tabo wasu batutuwa da suka shafi siyasa.

A zantawar da aka yi da shi, Alhaji Sule Lamido ya yabawa Nyesom Wike, amma ya ce akwai wasu ‘yan siyasa da suke zuga Gwamnan na jihar Ribas.

Sule Lamido yake cewa Nyesom Wike mutum ne mai kokari, amma yana da yarinta a kansa.

Kara karanta wannan

Osun: Mutanen Ministan Buhari sun taimaka mani ta bayen fage inji ‘Dan takaran PDP

Kamar yadda jigon ya bayyana, Wike ya ci burin zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa bayan Atiku Abubakar ya lashe zaben tsaida gwani.

A karshe ‘dan takaran shugaban kasar ya yi watsi da Gwamna Wike, ya dauko Ifenayi Okowa. Sule Lamido ya ce ya kamata Wike ya sallamawa zabin.

Wike ya dauki izina - Sule

Daily Trust ta rahoto Sule yana mai cewa abin da ya kamata shi ne Wike ya dauki darasi daga rayuwar siyasar Peter Obi da kuma Farfesa Yemi Osinbajo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sule Lamido
Tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido
Asali: Twitter

“Mun yi babban gangami na kasa, aka zabi Atiku. Wike ya yi takara ya sha kasa. Wike mutumin kirki ne mai kokari, amma akwai yarinta a tare da shi.”
“Akwai mutane da ke zuga shi, amma an wuce wannan maganar, ba yau aka fara ba. Anyi haka da Peter Odili, an yi Osinbajo, ya kamata ya dauki darasi."

Kara karanta wannan

Abdullahi Adamu: Ba za mu iya tilastawa kowa zama ko ficewa daga APC ba

- Sule Lamido

Rikicin cikin gida da takarar 'Dansa

A game da rikicin PDP, Legit.ng Hausa da ta saurari hirar, ta ji ‘Dan siyasar yana cewa rigima ba laifi ba ne a siyasa, ya sha alwashin za su dinke barakar PDP.

Sule Lamido ya yi alkawarin jam’iyyar PDP ba za su ba al’ummar Najeriya kunya a zaben 2023 ba, ya kuma ce zaben Osun alamar nasara ce a shekarar 2023.

Gawurtaccen ‘dan siyasar ya tabo batun takarar Mustapha Sule Lamido wanda yake neman zama gwamnan jihar Jigawa a zaben 2023 a inuwar jam’iyyar PDP.

“Babban laifi na a Jigawa shi ne haihuwa. Laifi ne mutum ya haifi yara? Wanene bai son yaransa? Wanene ba ‘dan wani ba ne?”

- Sule Lamido

A game da mutanen da suka fice daga PDP, suka shiga jam’iyyar NNPP, Sule ya taya su murna cikin gatse, ya ce sun samu ‘yanci daga yin bauta a gidansa.

Kara karanta wannan

Lauya ya ja-kunnen ‘Yan Najeriya a kan zaben Atiku Abubakar ya zama Shugabansu

Kwankwaso v Idahosa

A jiya aka ji labari ‘Dan takarar shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso ya gabatar da wanda yake so ya zama Mataimakin Shugaban kasa a jam’iyyar NNPP

Kwankwaso yace ana rufe jami’o’i da sauran makarantu na watanni, amma shugabanni su na kashe miliyoyi wajen sayen fam din takara a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng