Magoya bayan ‘Dan takaran Shugaban kasa sun zargi Gwamna da hana su yin taro

Magoya bayan ‘Dan takaran Shugaban kasa sun zargi Gwamna da hana su yin taro

Peter Obi Support Network ta na zargin Gwamnatin Kaduna da hana ta dakin da za su yi taro

Kungiyar POSN ta shirya taron Obi-Datti a Arewa House, amma aka ki ba su damar yin taron

A cewar kakakin kungiyar, Gwamna ne ya bada umarni a hana su wurin bayan sun biya kudinsu

Kaduna - ‘Yan kungiyar Peter Obi Support Network sun zargi Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da kokarin hana su gudanar da taron da suka shirya yi.

Punch ta rahoto mutanen Peter Obi Support Network suna cewa sun yi nufin yin wani taro domin tara magoya-bayan ‘dan takaran LP, Peter Obi a Kaduna.

Kamar yadda Mai magana da yawun bakin kungiyar, Kwamred Sani Altukry ya fada, an yi muffin yin wannan taro ne a gobe Talata, 19 ga watan Yulin 2022.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya kaddamar da Mataimaki, ya ce ya dauko wanda za su gyara Najeriya

Sani Altukry yake cewa sun so su yi taron ne a Arewa House domin samun damar tattaunawa da magoya bayan ‘dan takaran da mataimakinsa a jam’iyyar LP.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dalilin taron mu - Kwamred Sani Altukry

A cewar Altukry, taronsu bai da hadi da kamfe ko tallata ‘dan takara, illa iyaka za a samu damar da masu goyon bayan ‘dan takarar za su zauna da junansu.

Shugaban kungiyar yake cewa makasudin taron shi ne hada ‘Yan tafiyar Obi-Datti a karkashin inuwa daya domin hada karfi domin tunkarar zabe mai zuwa.

Peter Obi
‘Dan takaran Shugaban kasa a LP, Peter Obi Hoto: @Peter Obi
Asali: UGC

A jawabin da Altukry ya fitar a ranar Litinin, ya ce Mau girma Nasir El-Rufai ya umarci Manajan dakin taron na Arewa House da ya hana su yin zaman.

Altukry yake cewa hukumomin dakin taron ba su yi masu bayanin kwarai na dalilin hana su wurin ba, bayan sun biya kudi da nufin za su yi zaman a makon nan.

Kara karanta wannan

Don Tinubu ya zabi Musulmi: Jarumin Nollywood Kenneth Okonkwo ya fice daga APC

Daily Post ta ce uzurin da aka bada shi ne ba zai yiwu a gudanar da gangamin Arewacin Najeriya na kungiyar Peter/Datti yayin da sa’o’i 24 suka rage ba.

POSN ta fito tana cewa babu wanda ya isa ya tsaida tafiyar da suka dauko domin ta mutane ce. Zuwa yanzu ba mu ji martanin da Gwamnan Kaduna ya yi ba.

NNPP ta na kara yaduwa

Ku na da labari cewa jam'iyyar nan ta NNPP ta na kara yaduwa a Arewa maso gabas, tayi caraf da wasu manyan ‘Yan siyasa a jihohin Bauchi da kuma Taraba.

A makon da ya gabata Sanata Isa Hamma Misau ya shiga tafiyar Kwankwaso a NNPP, ‘Dan siyasar ne ya raba Abdul Ningi da Majalisar dattawa a zaben 2015.

Sanata Joel Ikenya da ‘Dan Majalisar Wakilan Tarayya da wani 'Dan majalisar dokokin Jiha a Taraba sun bar PDP, za su nemi takara a jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Labari mai zafi: Bayan kwanaki 103, an fito da wasu fasinjojin jirgin Kaduna-Abuja

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng