Shugaban APC: Sam ba na raina abokin hamayya, amma dole mu ci zabe a 2023

Shugaban APC: Sam ba na raina abokin hamayya, amma dole mu ci zabe a 2023

  • Ana ci gaba da shirye-shirye don tunkarar zaben 2023 mai zuwa, jam'iyyu na bayyana irin karfin ikonsu
  • Shugaban APC ya bayyana cewa, ba ya raina abokin hamayya komai kankantarsa, don haka akwai shiri a kasa
  • A bangare guda, gwamnan jihar Yobe ya bayyana kwarin gwiwar nasarar APC a zaben na 2023 da ake ta shirin yi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ba zai raina karfin ikon jam’iyyun adawa ba gabanin babban zaben 2023.

Adamu ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise ranar Lahadi 17 ga watan Yuli.

Sai dai, a bangare guda kuma ya bayyana kwarin gwiwar cin nasara a zaben na 2023 da za a gwabza nan ba da jimawa ba duk da kokarin jam'iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaba Buhari ya jawo muka rasa zaben Gwamna a Jihar Osun - Jagoran APC

Ba na raina abokin hamayya, inji shugaban APC Adamu
Shugaban APC: Sam ba na raina abokin hamayya, amma dole mu ci zabe a 2023 | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake zantawa da gidan talabijin din, Adamu ya ce:

“A gaskiya, ban taba raina karfin abokan hamayya na ba. Ba kuma zan yi haka ba a yanzu. Ba wannan ne karon farko da na zama shugaban jam’iyya ba.
"Na taba yin Sakataren jam’iyya, na kasance shugaban jam’iyya a matakin jiha. Na fuskanci zabuka: Na ci wasu, na rasa wasu. Ba ni da wani dalili ko kadan da zan yi shakkar abokin hamayya na.
“Mutumin kirki, wanda shi ne shugaban jam’iyyar PDP, abokina ne. Mun san juna tun kafin mu sami wadannan mukamai.
“Peter Obi, na san shi lokacin yana gwamnan jihar Anambra. Na ziyarce shi. Wadannan su ne mutanen da suke da manufa mai kyau, gwargwadon abin da na sani. Suna da tushe mai karfi. Ba ni da shakka game da hakan.
"Don haka, ba ni da wani dalili ko kadan da zan raina ikonsu na jagorantar mutanensu zuwa ga nasara."

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamna PDP a jihar Osun ya bayyana dalilin da yasa yayi tsallaken layi

Abin da suka rasa

Sai dai, Adamu ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyya mai mulki ta fi sauran jam’iyyun adawa tsari da shirin tunkarar zaben 2023 mai zuwa, rahoton The Nation.

Ya ce:

“Ina gaya muku cewa mun fi su tsari. Muna da yawan mabiya. Muna da rajistar mambobin jam’iyyar. Kuna iya tabbatar hakan. Wadannan sauran jam'iyyun ba su da shi.
"Ba na tunanin akwai wani yanayi da zai sa mu gaza cin zabe a 2023."

Tikitin Tinubu da Shettima mabudin nasara ne ga jam'iyyar APC, gwamna Buni

A nasa bangaren, gwamna Mai Buni na jihar Yobe ya yabawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, bisa zabin abokin takararsa, Kashim Shettima.

Kamar yadda Punch ya ruwaito, Buni, tsohon shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC, ya bayyana Shettima a matsayin wanda ya cancanta yayin da ya bayyana matakin a matsayin tikitin samun nasara ga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Saura kwana 2 zaben Osun, Jam’iyya ta sa ‘Dan takarar Gwamna ya janye takara

ata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Mamman Mohammed, gwamnan ya bayyana cewa matakin zai kara fadada jam’iyyar da kuma kara mata damar samun nasara a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.