Tsohon Gwamna ya yi wuf, ya goge maganar da ya yi a Facebook a kan zaben Osun

Tsohon Gwamna ya yi wuf, ya goge maganar da ya yi a Facebook a kan zaben Osun

  • Ogbeni Rauf Aregebsola ya bada umarnin goge maganar da aka yi a shafinsa na Facebook da Twitter
  • Ministan ya bayyana cewa tun farko ba da umarninsa aka yada wannan magana a kan zaben Osun ba
  • A halin yanzu, an goge jawabin a shafukan kuma tsohon Gwamnan ya yi kira ga mutane su yi watsi da sakon

Osun - Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregebsola ya yi amai ya lashe kan tofa albarkacin bakinsa a game da zaben Gwamnan da aka yi a jihar Osun.

Da farko tsohon Gwamnan ya yi magana a shafinsa na Facebook, kafin a je ko ina, sai ya yi maza ya goge sakon da ya fitar, yana cewa shi ba da yawunsa akayi ba.

Kara karanta wannan

Yadda Shugaba Buhari ya jawo muka rasa zaben Gwamna a Jihar Osun - Jagoran APC

The Cable ta rahoto cewa Rauf Aregebsola ya goge maganar da ya yi a karshen makon jiya, yace sam ba da umarninsa aka yi maganar a Facebook ba.

“Osun Le Tente”

A shafin Aregbesola, an ji ya jawo wata aya a cikin Injila wanda take bayani a game da karfin Kaddarar Ubangiji, wanda ta fi karfin burin wani ‘Dan Adam.

An tsakuro ayan ne daga Sura ta Daniel da ke cikin Littafin Bible da Kiristoci su ke bi. Ana zargin hakan martani ne a dunkule ga ‘yan jam’iyyar APC a Osun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan wasu ‘yan sa’o’i, sai aka nemi wannan magana a dandalin Facebook aka rasa, rahoton ya ce tuni Rauf Aregebsola ya bada umarnin a goge maganar.

Aregbesola Oyetola
Tsohon Gwamna Aregbesola tare da Gwamna Oyetola a 2018 Hoto: Fadar Shugaban kasa
Asali: UGC

Ministan cikin gidan ya nesanta kan sa daga wannan jawabi da aka yi da sunansa, baya ga haka, sai yake cewa bai bada umarnin fitar da maganar a shafinsa ba.

Kara karanta wannan

Labari mai zafi: An kwantar da Osinbajo a asibiti, Likitoci na shirin yi masa aiki

Da yake karin haske a Twitter, Aregbesola ya nuna bai san da abin da aka rika yadawa a shafukansa ba, ya yi kira ga mutane su yi watsi da maganar da suka gani.

Sola Fasure ya fitar da wannan jawabi da yawun bakin Ministan a yammacin Lahadi

Ba da umarni na ba - Minista

“An ankarar da ofishin Ministan harkokin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, cewa an yi karambanin rubuta sako a shafinsa na Twitter da Facebook
Da kimanin karfe 8:00 na safiyar Lahadi, 17 ga watan Yuli, 2022. Yanzu haka an goge wannan sako da Ministan bai bada umarnin a fitar da shi ba.
Ana kira ga mutane, musamman manema labarai, su yi watsi da maganar.”

- Rauf Aregbesola

Rikicin APC a Osun

Ku na da labari cewa an dauki tsawon lokaci, tsohon gwamnan na jihar Osun da yaransa ba su ga maciji da Mai girma Gboyega Oyetola a jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Ni Zan Ci Zabe, In Ji Oyetola Bayan Ya Kada Kuri'arsa

Rauf Aregebsola ya yi yunkurin hana magajinsa watau Gwamna Oyetola samun tikitin tazarce a APC, amma shi da ‘yan bangarensa ba su yi nasara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng