Yanzu Yanzu: Buhari ya yi martani yayin da Adeleke na PDP ya lashe zaben gwamnan Osun
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Ademola Adeleke murnar nasarar da ya samu a zaben gwamnan jihar Osun
- Buhari ya ce sakamakon zaben ya nuna wadanda mutanen jihar Osun ke so ya mulke su ta hanyar kuri'arsu
- Shugaban Najeriyan ya kuma jaddada aniyarsa ta gudanar da ingantaccen zabe a lokacin mulkinsa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala, Sanata Ademola Adeleke, murnar lashe zaben da ya yi.
A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, Shugaba Buhari ya bayyana cewa sakamakon zaben ya nuna wanda mutanen jihar ke so ya jagorance su.
Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa nasarar da aka samu wajen gudanar da zaben ya tabbatar da dattako da jajircewar dukkanin masu ruwa da tsaki.
Ya kuma kara jaddada aniyarsa ta gudanar da ingantaccen zabe a karkashin mulkinsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya wallafa a shafin nasa:
“Ina taya Sanata Ademola Adeleke, dan takarar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), murnar nasarar da ya samu a zaben gwamnan Osun. Mutanen Osun sun nuna wadanda suke so ta hanyar zaben.
“Wannan ita ce damokradiyya: A mutunta muradin mutane.
“Gudanar da zaben #OsunDecides2022 cikin nasara ya nuna dattako da jajircewar dukkanin masu ruwa da tsaki wajen karfafa gaskiya a tsarin zaben Najeriya.
“Zan ci gaba da jajircewa don barin tarihi na zabe na gaskiya a Najeriya.”
Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya lashe zaben gwamnan jihar Osun
A baya mun kawo cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP),Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.
Baturen zabe a jihar, Toyin Ogundipe, ne ya sanar da sakamakon zaben a safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, jaridar The Cable ta rahoto.
Adeleke ya samu kuri’u 403, 371 wajen lallasa babban abokin hamayyarsa Gboyega Oyetola na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ya samu kuri’u 375,027.
Asali: Legit.ng