Zaben Osun: APC ta ji kunya, Gwamna ya rasa akwatin gidan Gwamnati a hannun PDP
- Adegboyega Oyetola mai neman tazarce ba zai ji dadi da jin sakamakon zaben gidan gwamnati ba
- ‘Dan takaran da PDP ta tsaida, Ademola Adeleke ya doka Gwamna Oyetola a rumfar gidan Gwamna
- Takardar da malamin zabe ya sa wa hannu ya nuna PDP ta samu kuri’u 117, APC kuma ta na da 106
Osun - Mai girma gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola bai iya samun nasara a akwatin da aka kada a gidan gwamnati da ke Osogbo ba.
Rahoton da This Day ta fitar a ranar Asabar, 16 ga watan Yuli 2022, ya tabbatar da cewa jam’iyyar PDP ta lashe akwatin rumfar gidan gwamnati.
A halin yanzu ana zaben gwamna a jihar Osun, inda Adegboyega Oyetola yake neman tazarce.
Shi kuma Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar hamayya ta PDP yana kalubalantar Adegboyega Oyetola da APC, kamar dai yadda aka yi a 2018.
Sakamakon zaben da aka fitar a yammacin yau, ya nuna jam’iyyar PDP ce ta kawo akwatin Agowande da ke unguwar Oshogbo GRA, Osun.
Rahoton yake cewa sakamakon da jami’in zaben rumfar gidan gwamnatin, Nwachukwu Henrietta Chidinma, ya tattara ya tabbatar da nasarar PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam’iyyar PDP da ‘dan takararta watau Sanata Adeleke sun zo na daya, sun samu kuri’u 117.
Shi kuma Gwamna mai-ci, Adegboyega Oyetola ya tashi da kuri’u 106, ya zo na biyu. Sauran kananan jam’iyyu ba su iya yin tasari a zaben ba.
Tuni dai aka ji labari Gwamna Oyetola da mai dakinsa sun kada kuri'unsu a gida. Gwamnan ya nuna ya na sa ran zai lashe zaben na 2022.
Accord Party ta samu kuri’u biyu kacal a zaben gwamnan. Su kuma jam’iyyun APM da SDP sun samu kuri’a daya, ita ma PRP ta tashi da kuri’a.
Abin mamakin shi ne jam’iyyar hamayya ta PRP ba ta shiga zaben ba, domin kuwa an ruguza takarar wanda ya tsaya mata yayin da ake shirin zaben.
Asali: Legit.ng