Da Ɗuminsa: Jam'iyyar APC ta lallasa PDP a mazaɓar Ministan Shugaba Buhari

Da Ɗuminsa: Jam'iyyar APC ta lallasa PDP a mazaɓar Ministan Shugaba Buhari

  • Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, kuma ɗan takarar APC ya lashe rumfar Ministan harkokin cikin gida a zaɓen yau Asabar
  • Duk da saɓanin da ya shiga tsakanin masu faɗa a ji na APC a jihar, gwamnan ya samu nasarar lallasa PDP da kuri'u 164
  • A yau Asabar 16 ga watan Yuli, hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun

Osun - Gwamna Gboyega Oyetola na jihar Osun ya lashe rumfar zaɓe ta 1, gunduma ta 08, Isare Ifofin, ƙaramar hukumar Ilesa ta gabas a zaɓen gwamnan Osun da ya gudana yau Asabar.

Gwamnan wanda ke neman tazarce karkashin inuwar jam'iyyar APC ya samu kuri'u 164, yayin da babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke, ya samu kuri'u 134.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jam'iyyar PDP ta lallasa APC a sakamakon rumfar zaɓe ta farko da aka bayyana a Osun

Gwamna Oyetola.
Da Ɗuminsa: Jam'iyyar APC ta lallasa PDP a mazaɓar Ministan Shugaba Buhari Hoto: Punchng
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, nan ne rumfar da yake zaɓe kuma ba dan ya tsallake ba, da ya dangwala ta shi ƙuri'ar a yau.

Kafin hawa kujerar Minista, Aregbesola, ya shafe zangon mulki biyu a matsayin gwamnan jihar Osun kuma shi ne wanda gwamna Oyetola ya gaje kujerarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai manyan jigan-jigan jam'iyyar APCn biyu reshen jihar Osun sun samu saɓani game da tsagin da zai cigaba da jan ragamar jam'iyya a jihar.

Meyasa tsohon gwamnan ve kaɗa kuri'arsa ba?

Da yake martani kan rashin kaɗa kuri'ar tsohon gwamnan jihar tsawon zango biyu, mai taiimaka wa Ministan kan harkokin kafafen watsa labarai, Sola Fasure, ya bayyana cewa Aregbesola baya ƙasar ne shiyasa.

"Ministan harkokin cikin gida (tsohon gwamnan Osun), Ogbeni Rauf Aregbesola, ba ya nan," inji hadimin na sa, kamar yadda rahoton vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Gujewa Zaben Gwamna a Jiharsa Ya Shilla Jamus

A wani labarin kuma kun ji cewa Hukumar zaɓe INEC ta ƙara wa'adin yin katin zaɓe zuwa 31 ga watan Yuli, 2022

Hakan ya biyo bayan kawo ƙarshen shar'ar da take yi da SERAP, wacce Kotun tarayya ta yi watsi da ita.

INEC ta ce ta ƙara yawan awanni da ma'aikata zasu yi aiki kana ta ƙara ranaku zuwa kowace rana maimakon ranakun aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel