2023: Tsohon Sanata da tsohon Minista sun shiga NNPP a Jihohin Taraba da Bauchi

2023: Tsohon Sanata da tsohon Minista sun shiga NNPP a Jihohin Taraba da Bauchi

  • Sanata Isa Hamma Misau ya sanar da sauya-shekarsa daga jam’iyya mai mulki zuwa NNPP
  • A Taraba, jam’iyyar NNPP ta samu ‘Yan Majalisa biyu da tsohon Minista, Sanata Joel Ikenya
  • Yayin da ake shirin zaben 2023, NNPP ta su Rabiu Kwankwaso ta na kara shiga Arewa ta gabas

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bauchi - Siyasar jihar Bauchi ta na cigaba da canza salo yayin da Sanata Isa Hamma Misau ya sake canza-sheka, wannan karo zuwa jam’iyyar NNPP.

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta gani a Facebook, Isa Hamma Misau ya hadu da Rabiu Musa Kwankwaso a yammacin Alhamis, 14 ga watan Yuli 2022.

A haduwar Sanata Isa Misau da ‘dan takaran shugaban kasar na 2023, ya tabbatarwa Duniya shigarsa cikin jam’iyyar ta NNPP mai alamar kayan marmari.

Misau ya wakilci mazabar Bauchi ta tsakiya a majalisar dattawa a APC, daga baya ya shiga PDP.

Kara karanta wannan

2023: Na-hannun daman babban Ministan Buhari yana yi wa PDP aiki a maimakon APC

Isa Hamma Misau da Yakubu Dogara su na cikin wadanda suka bar PDP kwanakin baya, suka sake komawa jam’iyyar APC mai mulki da suka bari a da.

Yanzu NNPP ta na da Sanatoci masu-ci biyu daga Bauchi, Dauda Halliru Jika da Tijjani Gumau duk sun bada sanarwar ficewarsu daga jam'iyyar APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon Sanatan Bauchi
Isa Hamma Misau da Rabiu Kwankwaso Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

NNPP ta yi kamu a Taraba

A jihar Taraba kuma, akwai rade-radin cewa Hon. Rimamde Shawulu ya fita daga jam’iyyar PDP mai mulkin jihar, shi ma ya koma jam’iyyar adawa ta NNPP.

Yanzu haka Shawulu ne ‘dan majalisan mazabun Dunga/Takun/Ussa/Yangtu a majalisar tarayya. Shi ma ‘dan majalisar jiha, Hon. Nasir Tafida ya bi shi.

Haka zalika ta tabbata Joel Danlami Ikenya ya sauya-sheka zuwa NNPP. Ikenya babban ‘dan siyasa ne wanda ya nemi kujerar Gwamna sau uku a jihar.

Kara karanta wannan

PDP ta kai INEC Kotu, ta bukaci a haramtawa Tinubu, Peter Obi neman Shugaban kasa

Tsakanin 1992 zuwa 1993, Ikenya yana majalisar dokokin Taraba. A 1999 kuma aka zabe shi a matsayin ‘dan majalisar wakilan tarayya, ya zarce har 2007.

Har ila yau, Joel Danlami Ikenya ya rike kujerar Sanatan Kudancin jihar Taraba zuwa 2011. Daga nan ya fara neman zama Gwamna a PDP amma bai dace ba.

Da Darius Ishaku ya zama ‘dan takaran Gwamna a PDP, Ikenya ne aka zaba ya maye gurbinsa a gwamnatin tarayya, ya zama Ministan kwadago zuwa 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng