Kai Tsaye: Yadda Zaɓen Gwamnan Jihar Osun Ke Gudana Yau Asabar
A yau Asabar, 16 ga watan Yuli, 2022, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa wato INEC zata gudanar da zaɓen gwamna jihar Osun.
Wa'adin zangon farko na gwamna mai ci, Gboyega Oyetola, na jam'iyyar APC ya zo karshe kuma al'ummar jihar zasu fito su zabi wanda zai cigaba da jagorantar su na tsawon shekara hudu.
Yan takarar da ake ganin suna sahun gaba a zaɓen sune;
1. Gwamna mai ci, Gboyega Oyetola, na jam'iyyar APC wanda ke neman tazarce
2. Ademola Adeleke na jam'iyyar PDP
3. Yusuf Lasun na jam'iyyar Labour Party LP
4. Rasaq Saliu na jam'iyya mai kayan marmari NNPP
Legit.ng Hausa ta shirya zata kawo muku duk abinda ke gudana kama daga shirye-shirye, yadda zaɓen zai gudana har zuwa lokaci da bayan sanar da sakamako.
Yarjejeniyar zaman lafiya
A ranar Laraba jam'iyyu 13, da suka haɗa da manyan jam'iyyyu APC da PDP, suka rattaɓa hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya tare da alƙawarin zasu nisanci ta da yamutsi yayin da kuma bayan zaɓe.
Shugaban hukumar zaɓe, Farfesa Mahmud Yakubu, ya yi kira ga yan takara, jam'iyyu da sauran masu ruwa da tsaki a wurin taron cewa sa hannun su bai isa ba, abinda ya fi muhimmanci shi ne bin abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa.
Dan takarar PDP, Ademola Adeleke ya lashe zabe
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP),Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun.
Baturen zabe a jihar, Toyin Ogundipe, ne ya sanar da sakamakon zaben a safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, jaridar The Cable ta rahoto.
Adeleke ya samu kuri’u 403, 371 wajen lallasa babban abokin hamayyarsa Gboyega Oyetola na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda ya samu kuri’u 375,027.
Sakamakon karamar hukumar Oriade
A 60
AAC 66
ADP 382
APC 14189
LP 24
PDP 15947
Sakamakon karamar hukumar Ife ta kudu
APC= 12,481
LP= 28
PDP= 9,116
Sakamakon karamar hukumar Ife ta gabas
APC= 19,353
LP= 65
PDP= 18,071
Sakamakon ƙaramar hukumar Ife ta kudu
APC: 12,481
PDP: 9,116
Sakamakon ƙaramar hukumar Ede ta arewa
APC: 9,603
PDP: 23,931
Sakamakon karamar hukumar Ife ta arewa
A: 74
AAC: 70
ADP: 341
APC: 9,964
APM: 50
APP: 24
BP: 14
LP: 4
NNPP: 11
NRM: 18
PDP: 10,359
PRP: 35
SDP: 9
YPP: 37
ZLP: 10
Sakamakon ƙaramar hukumar Ede ta kudu
A: 38
AAC: 43
ADP: 226
APC: 5,704
APN: 25
APP: 20
BP: 18
LP: 16
NNPP: 15
NRM: 57
PDP: 19,438
PRP: 33
SDP: 11
YPP: 37
ZLP: 10
Sanata mai rawa ya yi nasara a garuruwa 5
Alkaluma sun tabbatar da cewa ‘Dan takaran PDP, Ademola Adeleke ya samu nasara a kananan hukumomi biyar a zaben Gwamnan jihar Osun.
Jaridar Daily Trust ta ce PDP ta samu galaba a kan APC a kananan hukumomi Atakumosa ta yamma, Ifelodun, Orolu, Odo-Otin da Osogbo.
Adeleke ya na da kuri’u 79,453, Gwamna Gboyega Oyetola APC ya samu kuri’u 69,031. Tazarar kuri’a 10, 400 aka samu daga kananan hukumomin.
Sakamakon ƙaramar hukumar Ayedade
APC: 14,527
PDP: 13,380
Sakamakon ƙaramar hukumar Ife Central
A: 202
AAC: 145
ADP: 374
APC: 17880
APM: 59
APP: 21
BP: 10
LP: 134
NNPP: 14
NRM: 29
PDP: 13532
PRP: 42
SDP: 50
YPP: 44
ZLP: 08
Tsagerun sun jawo an daina tattara kuri’u
Tsageru sun kawo matsala a yayin da hukumar INEC ta ke kokarin tattara sakamakon kuri’un zaben Gwamnan Osun.
Hakan ya faru ne a karamar hukumar Ife ta Gabas kamar yadda jaridar Premium Times ta fitar da rahoto da yamman nan.
A dalilin haka, ma'aikata sun dakatar da tattara sakamakon kuri’un da aka samu daga rumfunan zaben da ake da su a yankin.
Sakamakon karamar hukumar Boripe
A - 91
AAC - 82
ADP - 355
APC - 21205
APM - 56
APP - 25
BP - 05
LP - 04
NNPP - 07
NRM - 13
PDP - 7595
PRP - 24
SDP - 09
YPP - 32
ZLP - 07
Sakamakon karamar hukumar Olorunda
A: 208
AAC: 95
ADP: 460
APC: 18709
APM: 40
APP: 23
BP: 19
LP: 63
NNPP: 17
NRM: 30
PDP: 21350
PRP: 56
SDP: 46
YPP: 51
ZLP: 20
Sakamakon karamar hukumar Atakumosa ta gabas
APC: 6,601
PDP: 7,750
Sakamakon Karamar Hukumar Edjigbo
APC: 8,919
PDP: 11,878
A: 41
AAC: 44
ADP: 282
APM: 39
BP: 9
LP: 23
NNPP: 11
NRM: 30
PRP: 36
SDP: 15
Sakamakon karamar hukumar Odo-Otin
APC: 13,482
PDP: 14,003
Sakamakon karamar hukumar Orolu
A : 69
AAC: 55
ADP: 271
APC: 9928
APM:21
APP:14
BP: 15
LP: 32
NNPP: 04
NRM: 14
PDP: 10282
PRP: 18
SDP: 09
YPP: 23
ZLP: 10
Sakamakon karamar hukumar Iwo
APC 17,421
PDP 16, 914
Sakamakon karamar hukumar Ifelodun
AAC - 93
ADP - 487
APC - 16,068
APM - 45
APP - 13
BP - 07
LP - 18
NNPP - 13
NRM - 17
PDP - 17,107
PRP - 31
SDP - 12
YPP - 47
ZLP – 13
Sakamakon karamar hukumar Osogbo
AAC: 130
ADP: 617
APC: 22,952
APM: 55
APP: 47
BP: 18
LP: 79
NNPP: 22
NRM: 48
PDP: 30,401
PRP: 70
SDP: 62
YPP: 79
ZLP: 22
Sakamakon karamar hukumar ILA
APC- 11163
PDP- 13036
Sakamakon karamar hukumar Ilesa ta yamma
AAC: 77
ADP: 407
APC: 10,777
APM: 48
APP: 22
BP: 09
LP: 40
NNPP: 13
NRM: 16
PDP: 13,769
PRP: 45
SDP: 21
YPP: 33
ZLP: 20
Gudunmar (RA): Oke ObaII, karamar hukumar Iwo
AAC: 14
ADP: 78
APC: 1833
APM: 04
APP: 08
BP: 00
LP: 03
NNPP: 03
NRM: 05
PDP: 1489
PRP: 08
SDP: 03
YPP: 11
ZLP: 03
An fara tserewa APC
A sakamakon zaben da aka fitar zuwa yanzu, Ademola Adeleke ne a gaba, ya ba Gwamna Gboyega Oyetola na APC rata.
Adeleke ya na da kuri’u 67,892 shi kuma Oyetola ya samu 56,915. Rahoton Daily Trust ya ce akwai ratar kusan kuri’a 11, 000.
Hukumar INEC ta na cigaba da tattara kuri’u
PDP ta lashe karamar hukuma 1
Sanata Ademola Adeleke na PDP ne aka tabbatar a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Osun a karamar hukumar Atakumos ta Yamma.
INEC ta ce ‘Dan takaran yana da kuri’a 7750, Gwamna Gboyega Oyetola da jam’iyyar APC ne suka zo na biyu da ratar kuri’a 1, 149 da kuri’u 6601.
Gunduma ta 3, Olugun Agbaakin, Karamar Hukumar Ede ta Arewa
APC: 1676
PDP: 1694
Gunduma ta 3, Isale Oba 3, Karamar Hukumar Iwo
APC: 1237
PDP: 1656
Gunduma ta 6, Ikire F, Karamar Hukumar Irewole
APC: 1990
PDP: 1829
Gunduma ta 15, Oke Oba 2, ƙaramar hukumar Iwo
APC: 1833
PDP: 1489
Gunduma ta 10, ƙaramar hukumar Ede ta kudu
APC: 361
PDP: 1130
Gunduma ta 007 Molete 3, ƙaramar hukumar Iwo
APC: 1585
PDP: 1477
Gunduma ta 001 Ikire A, karamar hukumar Irewole
APC: 1509
PDP: 1120
Gunduma ta 001, ƙaramar hukumar Ede ta kudu
Adadin masu kaɗa kuri'a: 6273
Adaɗin waɗan da aka tantance: 3242
A: 9
AAC: 8
ADP: 20
APC: 679
APN: 3
APP: 1
BP: 2
LP: 2
NNPP: 0
NRM: 5
PDP: 2443
PRP: 2
SDP: 6
YPP: 2
ZLP: 0
Jumullar halastattun kuri'u: 3182
Kuri'un da suka ɓaci: 49
Gunduma ta 04 Atelewo, ƙaramar hukumar Olorunda
Masu kaɗa kuri'a: 7371
Waɗan da aka tantance: 2935
A: 19
AAC: 3
ADP: 24
APC: 1370
APM: 2
APP: 2
BP: 1
LP: 4
NNPP: 03
NRM: 3
PDP: 1443
PRP: 8
SDP: 02
YPP: 2
ZLP: 1
Halastattun kuri'u: 2875
Kuri'un da suka lalace: 60
Jumullan kuri'un da aka kaɗa: 2935
Gunduma ta 10, Eyindi/Ipirin, ƙaramar hukumar Ila
A- 04
AAC- 03
ADP- 19
APC- 675
APM- 02
APP- 00
BP- 00
LP- 00
NNPP- 00
NRM- 02
PDP- 825
PRP- 01
SDP- 01
YPP- 01
ZLP- 01
Sakamakon gunduma ta 11 a ƙaramar hukumar Atakumosa ta yamma
Adadin masu katin zaɓe - 2714
Adadin mutanen da aka tantance - 936
A- 2
AAC-4
ADP-10
APC-593
APM-1
APP-0
BP-1
LP-1
NNPP-0
NRM-2
PDP-288
PRP-3
SDP-0
YPP-2
ZLP-0
Jimullan kuri'un da aka kaɗa - 907
Ƙuri'un da ba'a jefa dai-dai ba - 17
Sakamakon gunduma ta 03 Ikeija II, Ife ta kudu LGA
Masu rijistar zaɓe – 3443
Masu kaɗa kuri'a da aka tantance – 1699
A: 01
AAC: 0
ADP: 27
APC: 821
APM: 03
APP: 0
BP: 0
LP: 01
NNPP: 01
NRM: 01
PDP: 801
PRP: 01
SDP: 0
YPP: 01
APC ta rasa gidan Gwamnati
Sakamakon zabe ya tabbatar da cewa akwatin da ke gaban gidan gwamnati ya fada hannun ‘Dan takarar jam’iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke.
Adeleke ya doke Gwamna Oyetola a rumfar gidan Gwamnati, PDP ta samu kuri’u 117, APC ta na da 106 yayin da ake cigaba da tattara sakamako.
Sakamakon rumfa ta 08, gundumar Oba Isale 2, Iwo LGA
APC: 73
PDP: 55
Gudunma ta 07, akwatin zabe ta 001, karamar hukumar Olorunda
ADP 03
APC 150
PDP 140
Akwatin Zabe na 017, Gundumar Alagba, Karamar Hukumar Osogbo
ADP - 02
APC - 89
A - 0
AAC - 0
PDP - 92
LP - 0
PRP - 0
Gwamna Oyetola ya lashe rumfar zaɓensa
Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola ya lashe zaɓe a rumfar zaben da ya ke kaɗa kuri'a da gagarumin rinjaye inda ya samu kuri'u 545.
Sakamakon zaɓe a rumfa ta 02, gunduma ta, 01, ƙaramar hukumar Boripe
APC - 545
PDP - 69
Sakamakon zaben rumfa ta 5, gunduma ta 4 a karamar hukumar Ilesa ta Gabas
Sakamakon zaben gwamnan jihar Osun daga rumfa ta 5 a gunduma ta 4; Itisan/Ogudu, karamar hukumar Ilesa ta Gabas.
A- 01
AAC-01
ADP- 04
APM-1
APC - 96
PDP - 59
PRP-01
Sakamakon zabe su na ta shigowa
- Sakamakon zabe daga karamar hukumar Ife ta Tsakiya
Akwati na 3 (Post Office)
ADP 02
APC 116
PDP 103
- Sakamakon zabe daga karamar hukumar Ife ta Kudu
Akodi Famoroti Ifetedo
Ikija 1
APP: 0
AAC: 0
ADP: 01
APC: 65
APM: 0
APP: 0
BP: 0
LP: 0
NNPP: 0
NRM: 01
PDP: 70
PRP: 0
SDP: 0
YPP: 0
ZLP: 0
- Sakamakon zabe daga karamar hukumar Ife ta Arewa
Garin Yakoyo, Ife
AAC- 01
ADP- 01
APC- 103
PDP - 113
LP- 02
NRM- 01
- Sakamakon zabe daga karamar hukumar Ilesa ta Yamma
APP - 01
AAC- 01
ADP - 03
APC - 89
PDP - 154
YPP - 01
Rumfa ta 2, cibiyar kasuwa ta Moro
Sakamakon zaben gwmanan jihar Osun daga rumfa ta biyu a cibiyar kasuwa ta Moro da ke karamar hukumar Ife ta Arewa.
A- 2
AAC- 0
ADP- 5
APC- 101
PDP - 129
Sakamakon zabe daga karamar hukumar Ede ta Arewa
Sakamakon zabe daga rumfar Oba da ke karamar hukumar Ede ta Arewa; PU 004, Ward 08, Isibo/Buari-Isolo:
APC: 44
PDP: 131
Gunduma ta 4, Akwatin Zabe ta 6, Karamar Hukumar Iwo
Sakamakon zabe daga Gunduma ta 4, Akwatin Zabe ta 6, Karamar Hukumar Iwo
ADP 07
PDP 178
APC 176
Gunduma ta 4, Akwatin Zabe ta 4, Karamar Hukumar Iwo
ADP 07
PDP 98
APC 46
LP 11
Sakamakon zabe
PU 004, Fajuyi Hall OAU, Gunduma ta 05, Iremo/Ajebamidele, Karamar Hukumar Ife Central
PDP: 28
APC: 29
Accord: 9
LP: 2
Sakamakom zaɓe daga runfunan zaɓe sun fara bayyana
PU 4: ƙauyen Elepo, gundumar Bode-Osi ta 008, Olaoluwa LGA
APC: 38
PDP: 96
AAC: 2
PRP: 01
YPP: 01
Masu rijistar zaɓe: 329
Kuri'un da aka kaɗa: 141
Kuri'un da suka lalace : 03
Sakamako: Runfar zaɓe ta 29, gunduma ta 008, Olorunda LGA
PDP - 91
APC - 39
ACCORD - 1
YPP - 1
ADP - 3
APM - 1
SDP – 1
Kuri'un da suka lalace: 02
Sakamako: Rumfar zaɓe ta 5, gunduma ta 5, salvation Army, Oke fia, Osogbo
APC- 121
PDP -196
ADP-2
ZLP-1
SDP-1
Accord- 4
AAC - 1
PU 004, Fajuyi Hall OAU, gunduma ta 05, Iremo/Ajebamidele, Ife Central LGA
PDP: 28
APC: 29
Accord: 9
LP: 2
Ma'aikatan INEC na jiran lokacin rufe zaɓe
Wani Hoto da The Cable ta wallafa ya nuna yadda wasu ma'aikatan wucin gadi da ke aikin zaɓe a jihar Osun suka fara gyangyaɗi yayin da suke jiran lokacin karkashe zaɓe a hukumance.
An ɗauki Hoton ne a Rumfar Zaɓe ta 008, gunduma ta 007 a Ipetumodu 2, ƙaramar hukumar Ife ta arewa a jihar Osun.
Jami'an tsaro sun kama 'yan daba da bindigu
Yayin da zaɓe ya yi nisa a jihar Osun, jami'an tsaro sun yi nasarar damƙe wasu yan daba ɗauke da bindigu da ake zargin suna shirin ta da zaune tsaye.
Kudi kawai suke karba, ban ga kowani kuri’a ba, jami’in jam’iyya ya koka
Jami’in wata jam’iyyar siyasa a jihar Osun ya koka kan cewa mutane na karbar kudi ne kawai amma basu kada kowani kuri’a ba.
A cikin wani bidiyo da jaridar The Cable ta wallafa a shafin Twitter an jiyo jami’in na magana a harshen Yarbanci inda yake tambayar mutane jam’iyyunsu.
Gwamna Oyetola ya jinjinawa INEC kan yadda ake zabe cikin lumana
Gwamnan jihar Osun kuma dan takarar jam’iyyar APC, Adegboyega Oyetola, ya jinjinawa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) kan yadda ake gudanar da zaben cikin lumana.
Ya bayyana hakan ne bayan ya kada kuri’arsa a zaben.
Mai nakasa zai kada kuri'a
Wani mai nakasa yayin da ake tantance shi domin ya kada kuri’arsa a zaben Gwamnan jihar Osun.
Hukumar INEC ta na amfani da na’urar BVAS ne wajen tantance fuskar masu kada kuri’a a zaben Gwamna.
An dauki hoton ne a Ikire, a karamar hukumar Irewole.
Hoto: @INECNigeria
Dan takarar APC, Oyetola da matarsa sun kada kuri'arsu
Gwamnan jihar Osun kuma dan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Gboyega Oyetola da matarsa sun kada kuri'arsu.
Gwamnan dai yana takara ne domin neman wa'adi na biyu na gwamnan jihar.
Tsohuwa mai shekaru 80 ta fito ta kada kuri’a
Wata tsohuwa mai shekaru 80, Sidikatu Yusuf ta bayyana cewa ta damu da ci gaban Osun, inda ta ce wannan ne babban dalilinta na fitowa domin kada kuri’a a zaben.
Mawaki Davido: Mutane sun ki yarda su siyar da kuri’unsu
Mawakin Davido Adeleke wanda ya kasance 'da a wajen dan takarar PDP a zaben gwamnan na Osun, ya yi ikirarin cewa masu zabe sun ki karbar kudi don sayar da kuri’unsu.
Rikici ya barke a wata runfar zaɓe
Bidiyon yadda jami'an tsaro ke kokarin kwantar da hankulan fusatattun masu kaɗa kuri'a a runfar zaɓe ta 002, gunduma ta 001, ƙaramar hukumar Atakumosa.
Dattijo Mai Shekaru Fiye Da 90 Ya Jefa Kuri'arsa a Zaben Osun
Mustapha Olatunji, wani dattijo wanda ya haura shekaru 90 ya jefa kuri'arsa a karamar hukuma Boripe, Gunduma ta 1, Akwatin zabe na 002 a zaben gwamnan Osun.
Olatunji ya bayyana cewa tun zamanin tsohon firimiyan yankin yamma, Obafemi Awolowo ya ke zabe.
Tsohuwa ta kada kuri'a
Dazu aka ji cewa wata tsohuwa mai shekara 92 a Duniya, ta kada kuri'arta a akwatin zaben da ke makarantar firamaren Baptist Primary School a Isore/Ikonifin.
Kamar yadda INEC ta bayyana, wannan Baiwar Allah ta yi zaben ne a akwati na biyu da ke rumfa ta shida a Isore/Ikonifin da ke karamar hukumar Ola-Oluwa.
Dan takarar PDP, Ademola Adeleke, ya kaɗa kuri'arsa
Ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam'iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke, ya jefa ƙuri'arsa a zaɓen gwamnan Osun da ke gudana yanzu haka.
Sanata Adeleke ya kaɗa kuri'arsa ne a runfar zaɓe ta 009, gunduma ta 002, Abongunde/Sagba, a ƙaramar hukumar Ede ta arewa.
An fara kada kuri'a a rumfar dan takarar gwamnan APC a Osun
Yanzu haka an fara kada kuri'a a zaben gwamnan Osun, a rumfa ta 02, unguwa ta 1, Popo, Iragbiji a karamar hukumar Boripe LGA.
Rumfar dai ita ce ta inda dan takarar gwamna a jam'iyyar APC a zaben jihar yake.
Jami'ai INEC sun fara tantance masu kaɗa kuri'a
Ana gab da fara jefa kuri'a yayin da mutum na farko ya gabatar da kansa ga jami'an wucin gadi domin tantance shi a PU 1, Ward 3, makarantar Methodist, karamar hukumar Atakumosa ta yamma, jihar Osun.
Jami'an wucin-gadi na INEC suna dub sunayensu a ofishin INEC
Jami'an wucin-gadi na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, wadanda suka hada da masu hidimar kasa, sun duba sunayensu a ofishin hukumar zaben dake kan titin Ilobu a karamar hukumar Osogbo domin sanin inda ake tura su aikin zaben.
Mutane sun fara fitowa kaɗa kuri'a
Tuni masu ƙaɗa kuri'a suka fara tururuwa runfunan zaɓe domin kaɗa kuri'un su. A runfar zaɓe ta 1, gundumar Alajue 5, Aisu yankin Ede, mutanen da suka fito na zaune yayin da jami'an INEC ke shirye-shirye domin fara jefa kuri'a.
Wasu Hotuna da jaridar Vangaurd ta tattaro sun nuna yadda masu kaɗa kuri'u ke zaune yayin da matasa yan bautar ƙasa ke shiryawa don fara aikin su na wucin gadi.
Jami'an tsaro sun mamaye muhimman wurare a Osun
Jam'an tsaron Najeriya da suka haɗa da Sojoji, Yan sanda, Dakarun Cibil Defence sun mamaye manyan muhimman wurare a ilahirin babban birnin Osun da kuma garuruwa masu iyaka.
Hukumar yan sanda ta girke dakaru 21,000 don tabbatar da komai ya tafi cinin tsaro yayin zaɓen kuma ta gargaɗi duk wani me shirin tada zaune tsaye ya nesanci runfunan zaɓe.
Haka nan kuma hukumar tsaro ta Cibil Defence wato NSCDC ta ce ta jibge dakaru 11,000 kuma ta tabbatar wa mazauna jihgar da cewa zasu samu kariya.
Zamu karɓi kuɗi, mu zaɓi wanda muke so - Mazauna Osun
Yayin da komai ya kankama na zaɓen gwamnan jihar Osun yau Asabar, wasu daga cikin mazauna jihar sun shaida wa manema labarai cewa zasu tabbata sun zaɓi ɗan takarar da suke so.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa aƙalla mutum miliyan 1,955,657 suka yi rijistar zaɓe kuma ake tsammanin zasu kaɗa kuri'un su a runfunan zaɓe 3,763 dake faɗin jihar.
Haka nan ana tsammanin mutane zasu fito zaɓe kwansu da kwarkwata fiye da yadda suka fito a zaɓen 2018 da ya gabata.
Wani mazaunin Osun, Kunle Ogundele, ya ce: "Mutane zasu yi tururuwa su fito duk da akwai ƙalubalen sayen kuri'a. Zamu karɓi kudin su, kuma mu dangwala wa wanda zuciyarmu take so."
Demola Ahmed, wani mazaunin jihar ya ce mutane zasu fito duk da matakan tsaron da aka jibge suke aiki sintiri don tabbatar da tsaro a cikin gari.
Jam'iyyar AD ta ayyana goyon bayan gwamna Oyetola
Jam'iyyar Alliance for Democracy (AD) ranar Jummu'a ta ayyana cikakken goyon bayanta ga tazarcen gwamna Gboyega Oyetola, ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan Osun.
Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa jam'iyyar AD na ɗaya daga cikin jam'iyyun siyasa a Najeriya da hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta soke rijistar su.
A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaba da Sakataren tsare-tsare, jam'iyyar AD ta umarci mambobinta, masoya da magoya baya su yi tururuwa don kaɗa wa Oyetola kuri'un su.
An jibge jami'an yan sanda a jihar Osun
Bidiyon jami'an hukumar yan sanda waɗan da aka tura yin aiki yayin zaɓen gwamnan jihar Osun wanda zai gudana gobe Asabar, 16 ga watan Yuli, 2022.
INEC ta kammala rarraba kayan zaɓe
Hukumar zaɓe INEC ta bayyana cewa ta gama shiri tsaf na gudanar da zaɓen gwamnan Osun, ɗaya daga cikin jihohin yankin kudu maso yammacin Najeriya.
Yayin da ya rage awanni a fita runfunan zaɓe, INEC ta ce tuni ta kammala rarraba kayayyakim zaɓe zuwa ƙananan hukumomin jihar guda 30 a gaban jami'an tsaro.
Jami'ar INEC, Hajiya Zainab Aminu, ta shaida wa BBC Hausa cewa sun gama raba kayayyaki da suka haɗa da takardun kaɗa kuri'a da na rubuta sakamako cikin nasara.
A cewarta, dukkan kayayyakin da suka tura zuwa kananan hukumomi 30 sun isa lafiya ba tare da samun wata matsala ba.
Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng
Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng