Musulmi da Musulmi: Kada ku yarda wani fasto ko limami ya fada maku wanda za ku zaba, Keyamo ga yan Najeriya
- Ministan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Festus Keyamo ya ja hankalin yan Najeriya gabannin zaben 2023
- Yayin da ake caccakar tikitin Musulmi da Musulmi na APC, Keyamo ya bukaci talakawan Najeriya da kada su yarda malaman addini su fada masu ga wanda za su zaba
- Karamin ministan kwadagon ya ce kokarin Tinubu ya kamata a duba lokacin da yake matsayin gwamna ba wai bangarancin addini ba
Karamin ministan kwadago da daukar ma’aikata, Festus Keyamo, ya ce kada yan Najeriya su bari malaman addini su juya su a tsarin zaben shugaban kasa na 2023.
A ranar Lahadi da ya gabata ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya sanar da tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa na zabe mai zuwa.
Sanarwar ta zo ne jim kadan bayan Ibrahim Masari ya janye a matsayin abokin takarar Tinubu na wucin gadi.
Tikitin Musulmi da Musulmin ya haddasa cece-kuce a tsakanin yan Najeriya wadanda ke kallon hakan a matsayin rashin adalci ga al’ummar Musulmi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayan sanarwar, Keyamo ya bayyana Shettima a matsayin abokin takara da ya dace da Tinubu.
Sai dai kuma, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya soki hukuncin inda ya bayyana shi a matsayin kuskure da rashin adalci.
Saboda haka, a cikin wasu jerin wallafa da ya yi a shafin Twitter a ranar Laraba, Keyamo ya bukaci yan Najeriya da su yi watsi da bangaranci na addini sannan su mayar da hankali kan nasara yayin gudanar da zaben 2023.
Keyamo ya ce:
“Kada wanda ya yaudare mu, a matsayinmu na talakawan Najeriya, imma fasto ko liman, kan wanda za mu zaba ko wanda ba za mu zaba ba bisa la’akari da addini.
“A bari muhawarar ya fara kan kokarin Bola Tinubu a matsayin gwamnan jihar Lagas amma ba wai batun tikitin addini daya ba.”
2023: Tinubu ya ci zabe ya gama, In ji tsohon dan takarar kujerar gwamna a Plateau
A wani labarin, tsohon dan takarar gwamnan jihar Plateau karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), David Victor Dimka, ya yi hasashen cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu ne zai lashe zaben 2023.
Dimka, wanda ya kasance tsohon kwanturolan hukumar kwastam a wata hira da manema labarai a garin Jos, ya ce Tinubu dan siyasa ne da ya yarda da hadin kai da ci gaban Najeriya a matsayin kasa daya, Leadership ta rahoto.
Ya bayyana cewa duba ga tarin nasarorinsa a siyasa, Tinubu mutum ne wanda ke da abun da ake bukata don inganta Najeriya, duba da irin ci gaban da ya samu wanda a cewarsa ya shafi dukkan bangarorin rayuwa a fadin kasar.
Asali: Legit.ng