2023: Na sanyawa Tinubu da Shettima albarka, in ji Ali Modu Sheriff

2023: Na sanyawa Tinubu da Shettima albarka, in ji Ali Modu Sheriff

  • Ali Modu Sheriff ya nuna goyon bayansa ga tikitin Tinubu/Shettima gabannin babban zaben 2023 mai zuwa
  • Sheriff wanda ya ce tuni ya sanyawa tsohon kwamishinan nasa da dan takarar shugaban kasa na APC albarka ya ce zai yi iya kokarinsa don ganin sun lashe zabe mai zuwa
  • Tsohon gwamnan jihar Bornon ya ce Kashim Shettima da kansa ya kira ya fada masa jim kadan bayan an sanar da shi batun

Tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, ya ce ya sanyawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima albarka.

Sheriff ya bayyana hakan ne a cikin sakon taya murna dauke da sa hannun Cairo Ojougboh, Darakta Janar na kungiyar kamfen din Ali Modu Sheriff.

Martaninsa na zuwa ne kimanin awa 24 bayan Tinubu ya sanar da Mista Shettima, tsohon gwamna kuma sanata mai ci a matsayin abokin takararsa, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban kasa: Jiga-jigan APC a arewa maso gabas sun jinjinawa APC da Tinubu kan zabar Shettima

Ali Modu Sheriff
2023: Na sanyawa Tinubu da Shettima albarka, in ji Ali Modu Sheriff Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Hukuncin Tinubu na zabar Musulmi dan uwansa a matsayin abokin takararsa ya haifar da cece-kuce.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan Najeriya da dama ciki harda kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) sun gargadi jam’iyyun siyasa kan fitar da yan takara daga addini guda amma Tinubu ya yi biris da haka.

A cikin sanarwar, Sheriff ya ce Shettima wanda ya yi aiki a matsayin kwamishina a karkashin gwamnatinsa, ya sanar da shi batun zabarsa jim kadan bayan ya samu labari, Daily Post ta rahoto.

Shettima ya yi aiki karkashin Sheriff a matsayin kwamishina a lokacin da yake matsayin gwamnan jihar Borno tsakanin 2003 da 2011.

Sheriff ya ce:

“Shettima da kansa ya sanar da ni batun zabarsa jim kadan bayan an sanar da shi, kuma na sanyawa tikitin Tinubu/Shettima albarka.
“Mun sanyawa shi da ubangidansa albarkarmu kuma mun umurci kowa ya kokarta yayin da muke aiki cike da hadin kai don tabbatar da nasarar jam’iyyar a 2023.”

Kara karanta wannan

Tikitin Tinubu da Shettima mabudin nasara ne ga jam'iyyar APC, gwamna Buni

Yayinda ya umurci dukkanin shugabanni da mambobin jam’iyyar da su yi aiki don tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben 2023, tsohon gwamnan ya bayyana cewa a shirye yake ya yi aiki a matsayin tawaga daya.

Ya kara da cewa:

“Zan yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ganin cewa APC ta lashe zabe mai zuwa.”

Mataimakin shugaban kasa: Jiga-jigan APC a arewa maso gabas sun jinjinawa APC da Tinubu kan zabar Shettima

A wani labarin, shugaban majalisar dattawa, Dr Ahmad Lawan, da manyan jiga-jigan APC a arewa maso gabas sun taya Sanata Kashim Shettima murnar zabarsa da aka yi a matsayin mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.

Shettima shine abokin takarar Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki.

Lawan, a wata sanarwa da ya fitar a madadin jiga-jigan yankin a Abuja a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli, ya ce Tinubu da APC sun yi zabi mai kyau a Shettima, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi da Musulmi: Kungiyar arewa ta jero abubuwa 3 da Tinubu zai fuskanta

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng