Kwankwaso: Idan na rasa kujerar Buhari, kowa ma ya rasa, amma Tinubu ya samu
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP ya bayyana yiwuwar mara wa Tinubu baya idan ya gaza samun damar cin zabe
- Ya bayyana cewa, ta san Tinubu mutumin kirki ne, kuma ya ce ya yi masa farin sani tun shekaru da dama da suka wuce
- A bangare guda, Kwankwaso ya kuma bayyana cewa, Tinubu na da dabarun siyasa kuma ba zai iya tafiya irin ta Buhari ba
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya ce zai marawa takwaransa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu baya, idan ya ga ba zai ka ga gaci ba a zaben 2023.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da yayi a gidan talabijin na Arise a daren Lahadi.
Tsohon gwamnan na Kano ya yi magana ne biyo bayan sanarwar da Tinubu ya yi na zabi Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa.
Ya yi ikirarin cewa yana da kyakkyawar alaka da shugaban na jam’iyyar APC na kasa a baya kuma ba zai raina karfinsa da dabarun tafiyar da al’amuran Najeriya ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar Vanguard ta rahoto lokacin da Kwankwaso ke magana game da zabi Shettima, ya ce:
“Na yi matukar farin ciki da hadin, abin da ke damuna kawai shi ne dandalin, na san Bola Tinubu mai dabara ne; mutumin kirki ne, na sami damar zama da shi sau da yawa, daga 1990 zuwa yau.
“Abin da kawai ban sani ba shi ne abin da zai gaya wa ‘yan Najeriya zai yi daban da abin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi. A ka’ida, idan ba zan samu ba (shugaban kasa) zan iya mara wa Tinubu baya."
Kwankwaso ga Tinubu: Ka bi a hankali, ka kula da lafiyarka, ka bar mu da kamfen
A wani bangare kuma, dan takarar shugaban kasan na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya shawarci Bola Tinubu, mai rike da tutar jam’iyyar APC da ya tafi ya kula da lafiyarsa.
Da yake magana a yayin wata hira da Reuben Abati na AriseTV a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, shugaban na NNPP ya ce yakin neman zabe yana da matukar tattare da kalubale kuma Tinubu yana bukatar sassautawa saboda lafiyarsa.
Ya ce: “Idan ka ga abokina, Bola, ka gaya masa ya bi hankali, kula da lafiyarsa sosai kuma ka tabbatar… saboda ina kaunarsa sosai, abokina ne.
Asali: Legit.ng