Shugaban kasa a 2023: Kwankwaso ya gamsu da hadin Tinubu da Shettima
- A ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a zaben 2023
- Kamar yadda ya bayyana a wata hira da aka yi da shi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya ce ya ji dadin wannan hadi sosai
- Kwankwaso ya bayyana tsohon gwamnan na jihar Borno a matsayin mutumin kirki kuma salihi
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli, ya nuna gamsuwa da zabin abokin takarar Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.
Asiwaju Bola Tinubu wanda ke rike da tutar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa.
A yayin wata hira da Arise News, Kwankwaso ya bayyana Shettima wanda ya kasance sanata mai wakiltan Borno ta taskiya a matsayin mutumin kirki.
Jaridar Punch ta nakalto Kwankwaso yana cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Shettima ya kasance takwarana a matsayin gwamna a lokacin wa’adin mulkina na biyu. Mutum ne salihi, mutumin kirki ne. Ina yi masa fatan alkhairi.
“Ina matukar farin ciki da hadin; damuwata itace dandalin (APC). Wannan dandalin… ban sani ba.
“Bola Tinubu mutum ne mai dabara. Na zauna da shi sau da dama saboda wasu dalilai tun daga 1992 har zuwa yau.
“Na so ace zan gan sa don na tambaye shi abun da zai yi da ya banbanta da wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi a yanzu. Wannan shine babban damuwata a gare shi.”
Kwankwaso ga Tinubu: Ka bi a hankali, ka kula da lafiyarka, ka bar mu da kamfen
A gefe guda, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya shawarci Bola Tinubu, mai rike da tutar jam’iyyar APC da ya tafi ya kula da lafiyarsa.
Da yake magana a yayin wata hira da Reuben Abati na AriseTV a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, shugaban na NNPP ya ce yakin neman zabe yana da matukar tattare da kalubale kuma Tinubu yana bukatar sassautawa saboda lafiyarsa.
Asali: Legit.ng