Atiku ya hakura da hutun da yake yi a kasar waje, zai dawo ganin babu lafiya a PDP
- Hankalin Atiku Abubakar bai kwanta da yadda ya ga APC na zawarcin Gwamna Nyesom Wike ba
- Rahotanni sun nuna Atiku Abubakar yana shirin dawowa Najeriya daga kasar waje da ya je hutu
- ‘Dan takaran shugaban kasan na jam’iyyar PDP zai jagoranci PDP wajen zaben Gwamna a Osun
‘Dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar yana shirin tattara komatsansa, ya baro kasar waje inda yake hutawa bayan samun tikiti.
Rahoton Daily Trust na ranar Litinin, 11 ga watan Yuli 2022, ya tabbatar da cewa Alhaji Atiku Abubakar zai dawo Najeriya saboda rikicin gidan PDP.
Wazirin Adamawa zai katse hutun da yake yi ne bayan ganin gwamnonin APC sun sa labule da Nyesom Wike, wannan sam bai yi wa ‘dan takaran dadi ba.
Wani na kusa da tsohon mataimakin shugaban kasar ya shaidawa jaridar Atiku Abubakar zai sa kafa a Najeriya ba da dadewa ba, ana sa rai yau ko gobe.
Zaben Gwamnan Osun
Idan Atiku ya dawo kasar nan, shi ne wanda zai jagoranci yakin neman zaben gwamnan jihar Osun. PDP za ta shiga garin Osogbo a ranar Alhamis mai zuwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da zarar shi (Atiku) ya hallara, zai jagoranci zaman tattaunawa da sasantawan da za ayi a sakamakon rikicin da ya barke bayan zaben tsaida gwani.
Majiyar
Jaridar ta nemi jin ta bakin Mai magana da yawun ‘dan takaran, Paul Ibe, wanda ya tabbatar da cewa mai gidansa zai taya Ademola Adeleke yakin neman zabe.
Gudun ayi irin na Ekiti
A rahoton da The Cable ta kawo, an tabbatar da cewa zaman Atiku Abubakar a nahiyar Turai zai zo karshe, yayin da ake shirin zaben Gwamna a jihar Osun.
Atiku da jiga-jigan PDP sun gamu da suka a watan da ya wuce saboda ba a gansu wajen taya ‘dan takaran jam’iyyar PDP yaki a zaben sabon Gwamnan Ekiti ba.
Biodun Oyebanji wanda APC ta tsaida ya lashe zaben, ya doke ‘dan takarar SDP, Segun Oni. Bisi Kolawole na jam’iyyar PDP ya zo na uku ne a wannan zabe.
Silar rikicin PDP shi ne tsaida Ifeanyi Okowa da Atiku Abubakar ya yi a matsayin abokin takara.
Wike ba zai bi APC ba
Kwanan nan aka ga Kayode Fayemi, Olurotimi Akeredolu, da Babajide Sanwo-na APC sun yi kus-kus da Nyesom Wike da Ayo Fayose a Fatakwal da ke jihar Ribas.
Kun ji labari Bukola Saraki ya ce Gwamnonin jihohin ba APC su yi su gama, Gwamnan Ribas, Nyesom Wike ba zai bar jam’iyyar PDP ana shirin zabe ba.
Asali: Legit.ng