Muhimman abubuwa 7 da ya dace a sani game da Kashim Shettima, abokin tafiyar Tinubu
- 'Dan takarar kujerar shugabancin kasa a karkashin APC, Bola Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin tafiyarsa
- Bayan Tinubu ya yi wannan sanarwar, 'yan Najeriya zasu so sanin karin bayani game da wannan 'dan siyasan haifaffan jihar Borno
- Shettima makusancin Tinubu kuma 'dan gani-kasheninsa, mai masa yakin neman zabe tun kafin ya ci zaben fidda gwani na jam'iyyar APC
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
A ranar Lahadi 10 ga watan Yulin 2022 ne 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da Sanata Kashim Shettima na Borno a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 mai zuwa.
Tinubu ya tabbatar da zabin Shettima a yayin zantawa da manema labarai a garinsu shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daura dake jihar Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan takarar jam'iyyar APC ya je har garin Daura ne domin mika gaisuwar sallah babba da aka yi a ranar Asabar ga shugaban kasa.
Legit.ng ta zakulo muku tare da nemo muku muhimman abubuwan da ya dace ku sani game da 'dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC a zaben 2023.
- An haifa Shettima a Maiduguri dake jihar Borno a ranar 2 ga watan Satumban 1966 a gidan Sir Kashim Ibrahim. A halin yanzu yana da shekaru 55 a duniya kuma kabilar Kanuri ne.
- Tsohon gwamnan jihar Borno ne wanda ya mulka jihar tsakanin 2007 zuwa 2015 kuma Sanata ne mai ci a yanzu wanda aka zaba tun 2015 domin ya wakilci mazabar Borno ta tsakiya a majalisar dattawa.
- Yana da digirinsa na farko daga jami'ar Maiduguri inda ya karanci tattalin arziki na harkar noma da kiwo kuma yayi digirin digo a wannan fannin daga jami'ar Ibadan.
- Ya yi hidimar kasarsa a tsohon bankin manoma na Najeriya dake Kalaba, babban birnin jihar Cross River daga 1989 zuwa 1990.
- Shettima ya koma jami'ar Maiduguri a matsayin malami mai koyarwa a sashin tattalin arziki na noma da kiwo kuma ya kwashe shekaru 2 yana aikin.
- Shettima kwarraren ma'aikacin banki ne kuma masani a fannin tattalin arziki kafin ya fada siyasa. Daga 2007 zuwa 2011, ya rike kwamishina a ma'aikatu biyar.
- Yana auren Nana Shettima kuma sun haifa yara uku. Mata biyu da yaro namiji daya.
Asali: Legit.ng