Yanzun nan: Shettima bai san shine abokin takarata ba, in ji Tinubu
- A ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya bayyana Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a zaben 2023
- Tinubu ya ce Shettima bai san da kwanan zancen ba har zuwa lokacin da ya sanar da manema labarai
- Tuni dai Alhaji Ibrahim Masari ya fitar da wasikar janyewa daga matsayin abokin takarar Tinubu na wucin gadi
Katsina - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu, a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, ya bayyana cewa bai sanar da tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, cewa shine ainahin abokin takararsa ba, jaridar Punch ta rahoto.
Jawabin Tinubu na zuwa ne kasa da sa’a daya bayan Ibrahim Masari ya sanar da janyewarsa daga matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasar na APC.
Babban jagoran na APC ya ayyana Shettima a matsayin da takarar mataimakin shugaban kasa yayin da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, jihar Katsina.
Ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Na ga Masari a yau kuma za a bayar da sanarwa don maye gurbinsa da dan takara na din-din-din.”
Da aka matsa masa ya bayyana wanene dan takarar na din-din-din, sai Tinubu ya bayyana cewa Shettima ne, koda dai bai tattauna batun da shi ba.
Ya ce:
“Kashim Shettima, ban tattauna da shi amma na fada maku.”
Tinubu ya samu rakiyar gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari zuwa Daura bayan ya sauka a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua, Katsina.
Masari ya janye daga matsayin abokin takarar Tinubu
Mun kawo a baya cewa Alhaji Ibrahim Masari ya janye daga matsayin abokin takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress(APC).
Masari ya tabbatar da hakan ne a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli.
Asali: Legit.ng