Da dumi-dumi: Tinubu ya dauki Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa
- Gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023, ta tabbata jam’iyyar APC tikitin Musulmi da Musulmi za ta yi
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa
- A yau Lahadi, 10 ga watan Yuli, za a je har Daura domin sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda Tinubu ya zaba ya zama mataimakinsa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Rahotanni da ke zuwa mana a yanzu sun nuna cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives (APC) a zaben 2023, Bola Tinubu, ya bayyana abokin takararsa.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a babban zaben mai zuwa.
Tinubu ya sanar da hakan ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, a garin Daura, jihar Katsina, yayin da ya kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari gaisuwar ban girma na babban Sallah, Channels Tv ta rahoto.
Shugaban kasa Buhari na a Daura tun a ranar Juma’a, domin yin bikin babban Sallah.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Idan za ku tuna, Shettima ya taka gagarumin rawar gani wajen yiwa Tinubu kamfen kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar.
Musulmi da Musulmi: Tinubu ya sake samun gagarumin goyon baya daga tsohon gwamna
A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja, ya bayyana cewa babu wani aibu wajen tsayar da Musulmi da Musulmi domin zama shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a babban zaben 2023.
Da yake magana a gidansa da ke Bodija, Ibadan jim kadan bayan sallar Idi, tsohon gwamnan ya ce bai kamata ra’ayin Musulmi da Musulmi ya zama cikas wajen zabar shugabanni ba, jaridar The Guardian ta rahoto.
Ya ce zabar dan takara da ya cancanta bai da alaka da makomar addinin mai shi.
Asali: Legit.ng