Babu batun hada-kai da NNPP: Peter Obi ya zabi Baba-Ahmed ya zama abokin takara
- Yusuf Datti Baba Ahmed ne zai zama ‘Dan takaran Mataimakin Shugaban kasa a jam’iyyar LP
- Bisa dukkan alamu, Sanata Datti Baba Ahmed ne wanda Peter Obi ya zaba su yi takara tare
- An janye Dr. Doyin Okupe a matsayin ‘dan takaran mataimaki, za a kaddamar da Baba-Ahmed
Abuja - A ranar Juma’a, 8 ga watan Yuli 2022, jam’iyyar Labour Party (LP) za ta kaddamar da ‘dan takararta na mataimakin shugaban kasa a 2023.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shugaban jam’iyyar LP, Julius Abure ya ce Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed ne zai zama abokin takarar Peter Obi.
Yusuf Datti Baba-Ahmed shi ne shugaban jami’ar Baze University da ke garin Abuja. Legit.ng Hausa ta fahimci ‘dan takaran kwararre ne a fannin tattali.
Kwanan nan aka ji gwamnatin tarayya ta ba shi lasisin kafa jami’ar Baba-Ahmed University a Kano. Sanata Baba Ahmed bai kai shekara 50 a Duniya ba.
Jigo a jam'iyyar PDP
Baya ga zamansa mai makaranta, ‘dan siyasar yana cikin manyan 'yan PDP. Baba-Ahmed ya nemi jam’iyyar ta ba shi takarar shugaban kasa a zaben 2019.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton da Vanguard ta fitar a jiya ya bayyana cewa tun Alhamis aka yi nufin za a kaddamar da Yusuf Datti Baba-Ahmed, amma sai hakan bai yiwu ba.
Dalili kuwa shi ne Peter Obi ya je Maiduguri, jihar Borno. An sa ran ‘dan takaran zai dawo Abuja tun a jiyan, amma sai aka daga tafiyarsa a jirgin sama.
Julius Abure yake cewa za a kaddamar da ‘dan takaran na zaben 2023 a sakatariyar jam’iyyar ta Labor Party a Garki II da ke babban birnin tarayya Abuja
Abure ya sanar da cewa rashin dawowar Obi da wuri ya sa aka dakatar da taron sai Juma’a.
Legit.ng Hausa ta na sane da cewa Yusuf Datti Baba-Ahmed ba bakon siyasa ba ne, ya taba zama 'Dan majalisa na yankin Zaria da Sanatan Arewacin Kaduna.
Datti Baba-Ahmed ya yi niyyar neman zama ‘dan takarar gwamnan Kaduna a jam’iyyar PDP a 2022, daga baya ya hakura da shiga zaben fitar da gwani.
Obasanjo da Peter Obi
Mun ji labari tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo bai tare da Atiku Abubakar, Bola Tinubu da Rabiu Kwankwaso, ya na goyon bayan Peter Obi ne.
Mahadi Shehu ya ce Obasanjo ya zo Arewa taka-nas da nufin tallatawa Dattawan Arewa ‘dan takaran da yake goyon bayan ya zama shugaban Najeriya.
Asali: Legit.ng