Mahadi Shehu ya fadi ‘Dan takaran da Obasanjo yake neman tallatawa a Arewa
- Mahadi Shehu ya ce makasudin zuwa Olusegun Obasanjo Arewa shi ne tallata takarar Peter Obi
- A wata hira da aka yi da shi, Mai kamfanin Dialogue Group ya ce Obasanjo yana tare da Obi
- Tsohon shugaban kasar yana kokarin ganin ‘dan takaran na LP ne ya yi galaba a zaben 2023
Kaduna - Shugaban kamfanin Dialogue Group a Najeriya, Mahadi Shehu, ya fito yana cewa Olusegun Obasanjo yana goyon bayan Peter Obi a 2023.
Da aka yi wata hira da shi a gidan talabijin na Arise, Mahadi Shehu ya ce Olusegun Obasanjo yana goyon bayan Peter Obi ya karbi mulki a zabe mai zuwa.
Fitaccen ‘dan kasuwar bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya ziyarci wasu dattawan Arewa kwanan nan ne domin ya tallata masu takarar Peter Obi.
Shehu ya ce maganar ‘dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar Labor Party ne ta sa Obasanjo ya baro gidansa a Ogun, ya hadu da Ango Abdullahi a Zaria.
Abin da Mai kamfanin na Dialogue Group bai sani ba shi ne, Ango Abdullahi ya karbi maganar. Amma ya ce Obasanjo ya gana da su Hakeem Baba Ahmed.
Obasanjo bai tare da Atiku da Tinubu
‘Dan kasuwar ya ce Farfesa Abdullahi bai tare da Atiku Abubakar na PDP domin kuwa tun farko shi aka yi tunanin zai zama mataimakin Obasanjo a 1999.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar Mahadi Shehu, babu yadda za ayi Obasanjo ya goyi bayan takarar Bola Tinubu saboda sabanin da suka samu a lokacin yana Gwamnan jihar Legas.
Obasanjo yana ganin akwai ta-cewa a game da nasaba da salsalar ‘dan takaran na APC, haka zalika ana ta ce-ce-ku-ce a kan batun takardun makarantar Tinubu.
Sannan ‘dan kasuwan ya ce tsohon shugaban kasan ba zai marawa Atiku Abubakar baya ba, domin tun asali babu jituwa tsakaninsa da tsohon mataimakin na sa.
A hirar da aka yi da Shehu a Arise TV, ya ce Obasanjo bai kuma goyon bayan ‘dan takaran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya yi masa Minista a 2003.
...To sai mene kuma - Obi
Daga baya Daily post ta rahoto Peter Obi yana mai cewa babu laifi saboda dattijon yana bin manyan yankin Arewa domin ganin ya yi nasara a zaben 2023.
Ana kishin-kishin Obasanjo bai goyon bayan manyan ‘yan takaran 2023, yana tare da LP. Obi ya ce ba laifi tsohon shugaban kasar ya nema masa albarkar manya.
Hattara Kwankwaso inji IPOB
Dazu nan ku samu rahoto Kungiyar Indigenous People of Biafra wanda mutane suka fi sani da IPOB sun ce da su da Peter Obi, hanyar jirgi dabam, na mota dabam.
Mai magana da yawun IPOB, Emma Powerful ya fito ya yi raddi ga Rabiu Kwankwaso bayan wasu kalamai da ya yi a game da ‘dan takaran jam’iyyar LP a 2023.
Asali: Legit.ng