Shugaban kasa a 2023: Bana son tsohon hannu ya zama mataimakina, na fi son matashi mai jini a jika, Peter Obi

Shugaban kasa a 2023: Bana son tsohon hannu ya zama mataimakina, na fi son matashi mai jini a jika, Peter Obi

  • Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi ya bayyana wanda yake so ya zama abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023
  • Obi na son ya yi takara ne tare da matashi mai jini a jika wanda ke da sabbin manufofi ba wai tsoffin hannu da suka dade a harkar siyasa ba
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar goyon bayansa suka nemi ya janye daga duk wata tattaunawa na kokarin kulla kawance tsakaninsa da Kwankwaso

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, a ranar Laraba, 6 ga watan Yuli, ya magantu a kan wanda yake so ya zama abokin takararsa a babban zaben 2023 mai zuwa.

Obi ya bayyana cewa idan son samu ne, ya fi kaunar matashi mai jini a jika ya zamo masa dan takarar mataimakin shugaban kasa, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan a mutun Peter Obi: A bar maganar maja tsakanin Kwankwaso da Peter Obi

Peter Obi
Shugaban kasa a 2023: Bana son tsohon hannu ya zama mataimakina, na fi son matashi mai jini a jika, Peter Obi Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a shirin safiya na gidan talbijin din Arise.

Ya kara da cewar ya fi son matashi wanda ke da abubuwan gabatarwa da za su tallafawa tikitinsa maimakon sake dauko tsoffin hannu wadanda suke dade a gwamnati.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan a mutun Peter Obi: A bar maganar maja tsakanin Kwankwaso da Peter Obi

A gefe guda, kungiyar goyon bayan Peter Obi ta nemi a gaggauta kawo karshen duk wasu tattaunawa da ke gudana na yunkurin kulla kawance tsakanin jam’iyyun Labour Party (LP) da New Nigeria Peoples Party (NNPP), jaridar Punch ta rahoto.

Koda dai NNPP ta ce tana tattaunawa da LP kan yiwuwar yin maja, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso ya jadadda cewa ba zai janye daga kudirinsa na neman shugabancin kasar ba.

Kara karanta wannan

Machina ya sanar da INEC cewa ana kokarin fitar da wasikar bogi kan janye wa Lawan

A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, 4 ga watan Yuli, kakakin kungiyar goyon bayan Peter Obi, Onwuasoanya Jones, ya ce bukatar kawo karshen irin wannan tattaunawar ya zama dole tunda Kwankwaso ya ce ba zai janye ba, jaridar The Cable ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng