Ba zamu duƙa mu roki Wike ba, inji Mamban BoT da ya gana da Gwamnan a Turkiyya

Ba zamu duƙa mu roki Wike ba, inji Mamban BoT da ya gana da Gwamnan a Turkiyya

  • Babban jigo a jam'iyyar PDP kuma mamba a kwamitin amintattu ya ce ba wanda zai duƙa ya rarrashi Wike kan abinda ya faru
  • Maina Waiziri ya ce Gwamnan jihar Ribas na bukatar ya zuba wa zuciyar ruwan sanyi domin matakin jam'iyya ya fi ƙarfin ra'ayin kowa
  • Ya kuma musanta jita-jitar cewa Atiku ne ya aike shi ya fara rarrashin Wike a Istanbul na ƙasar Turkiyya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Mamban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP, Adamu Maina Waziri, ya saɓa wa matakin jam'iyya na rokon gwamnan Ribas, Nyesom Wike kan zaɓen ɗan takarar mataimaki, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Rikii ya ƙi ci ya ƙi cinye wa a babbar jam'iyyar hamayya PDP tun bayan da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya zaɓi gwamna Okowa na Delta a matsayin abokin takararsa.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙura ba ta lafa ba, Amintaccen jigon PDP ya magantu kan ganawar Wike da Tinubu a Faransa

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike.
Ba zamu duƙa mu roki Wike ba, inji Mamban BoT da ya gana da Gwamnan a Turkiyya Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban BoT-PDP, Walid Jibrin, ranar Lahadi, ya ce jam'iyya zata tura tawagar wakilai da ya haɗa da Atiku, gwamna Okowa, Mambobin kwamitin ayyuka NWC, da BoT don sasantawa da Wike.

Amma tsohon ministan harkokiin yan sanda, Adamu Maina Waziri, ya yi watsi da matakin, inda ya bayyana matakin da gurguwar shawara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Maina ya ce:

"Gwamna Wike ya fusata kuma yana bukatar lokacin domin zuciyarsa ta yi sanyi kan abubuwan da suka faru. Na yarda a nemi sulhu amma inda muka raba jiha shi ne tura wakilai su duƙa masa."
"Duk shawarar da jam'iyya ta yanke, mambobi masu ɗa'a zasu yi biyayya, wajibi mu jingine kowane abu da ya faru a zaɓen fidda gwani mu tunkari gaba, jam'iyya ta zarce muradin kowannen mu."
"Da bakinsa Wike ya ce ba zai zama abokin takara ga kowa ba saboda haka dole mu nemi wani wanda zai aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ɗan takarar mu na shugaban ƙasa."

Kara karanta wannan

Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa

Shin dagaske Atiku ne ya tura shi ya gana da Wike?

A wata zantawa da BBC Hausa, Maina Waziri ya kuma yi watsi da raɗe-raɗin cewa Atiku Abubakar ne ya tura shi ƙasar Turkiyya a rarrashi gwamna Wike.

"Atiku be tura ni ko ina ba amma tabbas na je birnin Istambul na Turkiyya domin hutu na ranar Jumu'a kuma muka yi kiciɓis da shi a Hotel, abinda ya faru kenan."
"Mun gaisa kuma shi yasan akwai maganar da ya kamata na masa amma ban masa. Ba wani ɗan lele a PDP kuma ina da tabbacin ba inda zai je ya na nan darama a PDP."

A wani labarin kuma Wani gwamna ya shilla Faransa ya sa labule da Tinubu, Hoton su ya ja hankalin mutane

Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya garzaya har ƙasar Faransa ya sa labule da tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kujerar Shugaban PDP na lilo bayan sabon rikicin da ya barke kan abokin takaran Atiku

Duk da wata matsala da suka samu kafin zaɓen fidda gwanin APC, manyan yan siyasan biyu sun tattauna was u batutuwa a haɗuwarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262