Wani gwamnan APC ya ziyarci Bola Tinubu a ƙasar Faransa, Hoton su ya ja hankali

Wani gwamnan APC ya ziyarci Bola Tinubu a ƙasar Faransa, Hoton su ya ja hankali

  • Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya garzaya har ƙasar Faransa ya sa labule da tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu
  • Duk da wata matsala da suka samu kafin zaɓen fidda gwanin APC, manyan yan siyasan biyu sun tattauna wasu batutuwa a haɗuwarsu
  • Mako ɗaya kenan da ɗan takarar shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya tafi Faransa, ya ce wasu taruka suka kai shi

Hoton gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, da ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yanzu haka shi ke jan hankalin mutane a kafafen sada zumunta.

Tsohon gwamnan Legas ɗin ya fice daga Najeriya ne makon da ya gabata, tafiyar da ofishin yaɗa labaransa ya kira da, "Halartar wasu taruka masu muhimmanci" a ƙasar ta Turawa.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙura ba ta lafa ba, Amintaccen jigon PDP ya magantu kan ganawar Wike da Tinubu a Faransa

Gwamna Abidun da Tinubu.
Wani gwamnan APC ya ziyarci Bola Tinubu a ƙasar Faransa, Hoton su ya ja hankali Hoto: @dabiodunMFR
Asali: UGC

Da yammacin ranar Litinin, gwamna Abiodun na jihar Ogun ya sanya Hotonsa tare da Bola Tinubu a shafinsana dandalin sada zumunta wato Tuwita.

A rubutun da ya yi kan Hoton, Gwamna Abiodun ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na shafe wasu lokuta tare da jagoran jam'iyyar mu kuma ɗan takarar shugaban ƙasa @OfficialABAT domin tattauna wasu batutuwa da suka shafi jam'iyyarmu da ƙasa."

Ya alaƙar manyan jiga-jigan siyasar take?

Manyan yan siyasan biyu sun ja hankali a kanun labarai watan da ya gabata yayin da Tinubu ya zargi Abiodun da laifin ƙin goya wa takararsa baya.

Bola Tinubua ya fito ya kira gwamna Abiodun da, "Eleyi," kalma a yaren yarbawa wacce ta ke nufin 'Wannan mutum ɗayan' inda ya ƙara da cewa ba don taimakonsa ba da bai zama gwamna ba.

A wani lokacin masu amfani da yaren na amfani da ita ta hanyar tausaya wa ƙimar wani mutum.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sako ma'aikatan lafiya, sun maida miliyoyin kuɗin da aka kai musu a Zamfara

Sai dai mako ɗaya bayan Tinubu ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa, shi da Abiodun sun haɗu a jihar Ekiti yayin yaƙin neman zaɓen Abiodun Oyebanji, sabon zaɓaɓɓen gwamna, wanda a lokacin yake ɗan takara.

A wani labarin kuma Jami'an tsaro sun mamaye majalisar dokokin jihar Bauchi bayan an yi yunkurin konata da dare

Yunkurin mafi rinjayen mambobin majalisar dokokin Bauchi na tsige kakaki, Abubakar Suleiman, ya gamu da cikas ranar Litinin yayin da jami'an tsaro suka kwace iko da zauren majalisar.

Punch ta ruwaito cewa rikicin da ya balle a majalisar kan shugabanci ya ɗauki sabon salo bayan wasu bara gurbi sun yi yunƙurin kone zaure majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel