2023: Tattaunawar haɗa kai tsakanin jam'iyyar LP da NNPP ta rushe, Victor Umeh

2023: Tattaunawar haɗa kai tsakanin jam'iyyar LP da NNPP ta rushe, Victor Umeh

  • Duk da ikirarin Kwankwaso cewa ana samun cigaba, Victor Umeh ya ce tuni tattaunawar kawaccen LP da NNPP ta rushe
  • Tsohon shugaban APGA kuma ɗan takarar Sanata a LP, ya ce tattaunawar ta ƙare ne tun 15 ga watan Yuni, kusan mako uku baya
  • Ya ce sun yi mamakin yadda mambobin NNPP ke cigaba da ikirarin cewa ana samun cigaba a batun kawancen

Abuja - Tsohon shugaban jam'iyyar APGA, Victor Umeh, ya bayyana cewa tattaunawar haɗin guiwa tsakanin jam'iyyun LP da NNPP ta ƙare tun ranar 15 ga watan Yuni.

Umeh, wanda ke neman kujerar Sanata karkashin jam'iyyar LP ya ce tattaunawar, "Ta rushe baki ɗaya," saboda kowane ɓangare ya ƙi yarda da wanda zai zama ɗan takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Wani gwamna ya shilla Faransa ya sa labule da Tinubu, Hoton su ya ja hankalin mutane

Tsohon shugaban na APGA ya faɗi haka ne a cikin shirin 'Sunrise Daily' na kafar Talabijin Channels tv ranar Talata.

Victor Umeh.
2023: Tattaunawar haɗa kai tsakanin jam'iyyar LP da NNPP ta rushe, Victor Umeh Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Umeh ya yi watsi da kalaman ɗan takarar jam'iyya mai kayan marmari, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya nuna cewa har yanzun ana cigaba da tattauna wa tsakanin ɓangarorin biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Cable ta ruwaito Ɗan takarar sanatan na LP ya ce:

"Muna mamakin yadda mambobin NNPP ke sakin baki a kafafen watsa labarai suna nuna cewa ana cigaba da tattaunawa da Labour Party don yin maja ko suna shirye-shiryen aiki tare a zaɓen 2023."
"Muna mamakin ganin kanun labarai kan haka, mun zauna a ranar 15 ga watan Yuni. Abun da muke gani shi ne idan LP da NNPP suka yi aiki tare zai ba da damar lashe zaɓen shugaban ƙasa, kowane ɓangare ya haɗa wakilai."

Kara karanta wannan

Zamfara: Matar shugaban ma'aikata da aka sace ta haihu a sansanin 'yan bindiga, ta kira shi a waya

"Ni, Julius Aboreh da shugaban LP wanda ya jagorance mu, Sai Doyin Okupe ya je wurin taron a madadin LP yayin da NNPP ta wakilta Buba Galadima, tsohom shugaban TETFUND, Abdullahi Baffa, da Ladipo Johnson."

Yaushe tattaunawar ta rushe baki ɗaya?

Victor Omeh ya ƙara da cewa kowane ɓangare ya haɗa wakilai mutum uku, kuma an haɗu wurin tattauna wa aka ɗage kuma aka sake dawo wa.

"A ranar 15 ga watan Yuni baki ɗaya tattaunawar ta rushe. Jami'iyyar LP ta ja baya ta nesanta kanta da duk wata tattaunawa da jam'iyyar NNPP. Amma sun cigaba da nuna cewa suna tattauna wa da LP."
"Mun gaza cimma matsaya kan wa zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi ko Rabiu Kwankwaso? Abin da suke faɗa mana ba zai yuwu ba a zahirance."
"Idan Peter Obi, wanda ake biɗarsa, ya janye domin ya koma mataimakin Kwankwaso, hakan zai zubar masa da ƙima da suna."

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya magaantu kan sabon rikicin da ya ɓarke a PDP, ya faɗi matakan da suke ɗauka

A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban ƙasa ya nesanta kansa da wani Hoto da aka ɗora shi kan daddumar Sallah

Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban kasa a 2023 ya nesanta kansa da Hoto da aka hangesa kan dardumar Sallah.

Peter Obi ya ce Hotonsa da wasu suka ɗora kan sallayar Sallah ba dai-dai bane ko da kuwa sun yi da kyakkyawar niyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262