Mai dakina ta na ajiye Bible dinta a gefen Qur’ani na, kuma a kwana lafiya inji Tinubu
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nuna bai samun jayayya da mai dakinsa saboda sabanin addini
- Sanannen abu ne cewa ‘Dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2023 yana auren Kirista ne
- Sanata Remi Tinubu za ta ajiye Bibble dinta a gefen Kur’anin Mai gidanta a daki, kuma babu rikici
‘Dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ajiye batun siyasa a gefe, ya yi maganar gidansa.
Legit.ng ta rahoto cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana abin da yake faruwa tsakaninsa da mai dakinsa, Sanata Remi Tinubu.
A wata magana da aka yi a Facebook a ranar Alhamis da ta gabata, ‘dan takaran shugaban kasar ya nuna irin zaman lafiyan da suke yi.
Joe Igbokwe, wanda yana cikin manyan magoya bayan tsohon gwamnan na Legas, ya yada wannan labari a shafinsa na Facebook.
Duk da Oluremi Tinubu Kirista ce, shi kuma mai gidan na ta Musulmi ne, ko kadan wannan bai hana su zama lafiya a gidan aurensu ba.
A cewar Tinubu, kowanensu yana ajiye Littafi mai tsarkin da ya yi imani da shi a cikin daki, ba tare da hakan ya kawo wata rigima ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto Tinubu yana cewa Kur’aninsa da Injilar mai dakin na sa, su na zamansu lafiya kullum.
Ga Bible, Ga Kur'ani - Tinubu
“A uwar dakanmu, matata ta na ajiye Injilarta a gefen Al-Kur’ani na.
Kuma abin da na gano shi ne, duka littatafan su na zamansu cikin zaman lafiya, ba tare da jayayya ba.”
Masu fashin baki za su ce abin da Tinubu yake kokarin nunawa shi ne saukin kansa da girmama addinin juna a matsayinsa na Musulmi.
Sanata Tinubu rikakkiyar Kirista ce da ta kai matsayin Fasto a Legas, a 2018 ne aka tabbatar da ita a matsayin Limamiya a wani cocin RCCG.
Shahara a shafin sada zumunta
Ku na da labari cewa bincike ya nuna Atiku Abubakar shi ne ‘dan siyasan da ya fi kowa yawan mabiya a shafin Twitter a fadin Najeriya.
An lura Muhammadu Buhari yana bayan Atiku Abubakar ne domin mutum miliyan 4.14 suke bin shi, amma Atiku ya na da mabiya miliyan 4.3
Asali: Legit.ng