Oshiomhole ya karbi tsohon hadimin gwamnan Edo zuwa jam'iyyar APC
- Tsohon shugaban jam'iyya mai mulkin Najeriya, Adams Oshiomhole, ya tarbi tsohon hadimin gwamnan Edo zuwa APC
- Tsohon gwamnan ya yaba wa shugaban kasa da gwamnonin arewa bisa amincewa mulki ya koma kudu
- Ya ce lokaci ya yi mamboɓin APC a Edo zasu haɗa kan su, su kwace mulki daga hannun PDP
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Edo - Tsohon shugaban APC na ƙasa, Kwamaret Adams Oshiomhole, ya karɓi tsohon mashawarcin gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo kan harkokin siyasa, Ogljo Asein, zuwa jam'iyyar APC.
Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar Edo, ya yi kira ga 'ya'yan APC a faɗin jihar su haɗa kai wuri guda domin jam'iyyar ta cigaba da mulkin Najeriya a 2023, kana ta kwace mulkin Edo daga hannun PDP.
Vanguard ta rahoto cewa Oshiomhole ya yi amfani da taron karban dandazon masu sauya shekan wurin nuna jin daɗinsa da ayyana Bola Tinubu, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na APC.
Haka nan kuma tsohon gwamnan ya yaba wa gwamnonin cigaba na APC na yankin arewacin Najeriya da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, waɗan da suka amince mulki ya koma kudu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake jawabi a wurin gangami a Sabongida-Ora, hedkwatar ƙaramar hukumar Owan ta yamma, Oshiomhole ya ce:
"Mun zo nan mu tarbi kuma mu sake ba da kyakkyawan wurin a gidan mu na siyasa ga ɗa na, Ojo Asein, da sauran dandazon mutanen da suka sauya sheƙa tare da shi."
Zamu kwace Edo mu ɗora daga inda muka tsaya - Oshiomhole
Ya yaba wa hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) bisa yunkurinta na sa ido kan murɗiya a zaɓe kana ya roki mutane su tabbata sun yi rijista sun karɓi katin zaɓe.
"Ƙimar shugaba ya rike alkawarin da ya ɗauka, ina tabbatar muku cewa zamu sake dawowa kuma mu ɗora daga inda muka tsaya, Edo zata bunƙasa. Haɗin kai zai bamu nasara, yanzu kan mu a haɗe yake."
A wani labarin kuma Wani gwamnan APC ya ziyarci Bola Tinubu a ƙasar Faransa, Hoton su ya ja hankali
Hoton gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, da ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu , yanzu haka shi ke jan hankalin mutane a kafafen sada zumunta.
Tsohon gwamnan Legas ɗin ya fice daga Najeriya ne makon da ya gabata, tafiyar da ofishin yaɗa labaransa ya kira da, " Halartar wasu taruka masu muhimmanci " a ƙasar ta Turawa.
Asali: Legit.ng