Gwamnatin tarayya ta yi gaggawar zargin ISWAP Kan Harin Cocin Owo - Akeredolu

Gwamnatin tarayya ta yi gaggawar zargin ISWAP Kan Harin Cocin Owo - Akeredolu

  • Akeredolu ya ce gwamnatin tarayya ta yi gaggawan daura wa kungiyar ISWAP alhakin harin cocin Owo
  • Gwamnan Jihar Ondo yace Fulani makiyaya, yan fashi da yan kungiyar ISWAP dake zama a dazuzukan su ke haifar da barna
  • Akeredolu ya nemi jam'ian tsaro su basu shaidan da ya sa suka yi gaggawa baiwa kungiyar ISWAP alhakin harin Owo

Jihar Ondo : Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo ya sake kin amincewa da gwamnatin tarayya akan wanda ya dace a dorawa alhakin kashe masu ibada a garin Owo.

Da yake jawabi akan kisan, a wata hira ta musamman da yayi da gidan talabijin na Channels Television's, ya ce alakantar da harin cocin Owo ga kungiyar ISWAP ya nuna akwai lauje acikin nadi. Rahoton ChannelTV.com

"Na tambaye su ko wace shaida suke da shi," in ji gwamnan. “Yana da mahimmanci a sanar da mu saboda jami’an tsaro sun yi saurin daurawa kuniyar ISWAP alhakin harin.

Kara karanta wannan

Hadimin gwamna ya tsallake rijiya da baya a hannun yan bindiga, ya bayyana halin da ya shiga

OWO K
Gwanatin tarayya ta yi saurin zargin ISWAP Kan Harin Cocin Owo - Akeredolu Foto LEADERSHIP
Asali: UGC
"Amma duk abin da yake, mun tsaya kan matsayin cewa kungiyoyi uku ne ke aiki a cikin dazuzzukan mu kuma shi haifar da barna. Akwai Fulani makiyaya, akwai ‘yan fashin, sai kuma yan kungiyar ISWAP; su ukun suna aiki tare kuma sukan yi aiki daban daban,” Inji shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Akalla mutane 40 ne suka mutu wasu da dama kuma sun jikkata a lokacin da ‘yan bindiga suka bude wuta kan masu ibada a Cocin St Francis Catholic dake Owo, hedikwatar karamar hukumar Owo ta jihar Ondo.

Lamarin da ya faru a ranar 5 ga watan Yuni wanda ya haifar da tofin Allah tsine

Kungiyar da ta sayawa Tinubu Fom din N100m, ta ce Elrufai take goyon bayan ya zama mataimaki

Jihar Kaduna, Gabanin wa'adin ranar 17 ga watan Yuli da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ba wa jam'iyyun siyasa su mika sunayen 'yan takararsu a zaben 2023, kungiyar TSO ta amince da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya zama mataimakin dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, kamar yadda ChannelsTV ta rwaito.

Kara karanta wannan

Saba alkawari: Ta karewa APC a Sokoto, 'yan kasuwa sun yi watsi da ita sun koma PDP

Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa ne a jam’iyyar APC mai mulki, ya fito fili ya ce har yanzu yana neman abokin takararsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel