Kujerar Shugaban PDP na lilo bayan sabon rikicin da ya barke kan abokin takaran Atiku
- An soma yada jita-jita cewa an tunbuke Dr. Iyorchia Ayu daga matsayinsa na shugaban PDP na kasa
- Rade-radin na nuna bayan sauke Dr. Iyorchia Ayu, har Amb. Umar Damagum ya maye gurbin na sa
- Ayu yana na a kan kujerarsa, amma babu shakka akwai masu huro wuta lallai sai an yi waje da shi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Nigeria - Rigimar da ta barke a jam’iyyar PDP bayan zaman Gwamna Ifeanyi Okowa ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa na 2023 na kara rincabewa.
Rahoton da Daily Trust ta fitar a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni 2022, ya nuna cewa lamarin ya kai ga ana kiran a sauke shugaban PDP, Dr. Iyorchia Ayu.
Masu neman a tunbuke shugaban jam’iyyar adawar na kasa, har sun soma yada jita-jitar an sauke shi. Tuni sakatariyar jam’iyyar PDP ta karyata labarin nan.
Hadimin shugaban jam’iyyar na PDP, Simon Imobo-Tswam ya ce Iyorchia Ayu bai sauka daga kujerarsa, har Amb. Umar Damagum ya karbi matsayin ba.
Iyorchia Ayu ya tafi hutu ne
Wani jawabin da Debo Ologunagba ya fitar ya ce Ayu ya dauki hutun makonni biyu ne daga ranar 21 ga watan Yuni, kuma zai dawo bakin aiki a makon gobe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun bakin shugaban jam’iyyar ta PDP ya yi kira ga musamman masu amfani da kafofin sada zumunta na zamani su daina biyewa jita-jita.
Mataimakin shugaban PDP na shiyyar Arewacin Najeriya, Amb. Umar Damagum yana rike da kujerar ne kafin Ayu ya dawo ofishinsa a ranar 6 ga watan Yul.
Gwamnonin PDP su na bore
Sabanin da aka samu a PDP ya fito fili wajen rantsar da kwamitin yakin neman zaben gwamnan Osun, gwamnoni biyu suka iya halarta a cikin goma da aka kira.
Shugaban rikon kwarya na PDP, Amb. Umar Damagum ne wanda ya rantsar da kwamitin, ya kuma yi kira gare su da su yi kokarin karbe jihar daga hannun APC.
Gwamnonin jihohin da aka gani su ne shi Ifeanyi Okowa da Gwamnan Taraba, Darius Ishaku. Ragowar gwamnonin sun kauracewa gayyatar da aka yi masu.
Masu hasashe da fashin baki su na ganin wannan rikicin cikin gida ya taimaka wajen kawowa PDP cikas a zaben sabon gwamnan jihar Ekiti da APC ta yi nasara.
Dauko Okowa ya kawo rikici
Ku na da labari cewa wanda zai rike kujerar takarar Mataimakin Shugaban kasa ya zama abin rigima a PDP, na-kusa da Gwamna Nyesom Wike sun tada rigima.
Da yake magana a jiya, Atiku Abubakar ya nuna zai sasanta da Nyesom Wike da ire-irensa ta hanyar lalama domin ganin ya doke jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng