Ba zan zabi Bola Tinubu ba, Peter Obi zan yi – Jagoran Jam’iyyar APC ya bada uzirinsa

Ba zan zabi Bola Tinubu ba, Peter Obi zan yi – Jagoran Jam’iyyar APC ya bada uzirinsa

  • Cif Jude Agbaso ba zai zabi jam’iyyarsa ta APC a zaben shugaban kasa ba saboda an hana su tikiti
  • Tsohon mataimakin gwamnan na jihar Imo yana ganin Ibo ya kamata ya karbi shugabanci a 2023
  • A kan wannan ne Agbaso zai zabi APC a zaben jiha, amma kuma zai dangwalawa Peter Obi na LP

Imo - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Cif Jude Agbaso ya fito ya shaidawa Duniya cewa Peter Obi ne zabinsa a zaben shugaban kasa na 2023.

Duk da yana cikin manyan jam’iyyar APC a kudancin Najeriya, The Guardian ta rahoto Cif Jude Agbaso yana cewa ba zai ba Bola Tinubu kuri’arsa ba.

Agbaso ya ce ‘dan takarar jam’iyyar Labor Party watau Peter Obi zai marawa baya a zabe mai zuwa, ya kuma fadi dalilinsa na daukar wannan mataki.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu

Jagoran jam’iyyar mai mulki a Najeriya ya ce rashin tsaida ‘dan takarar shugaban kasa daga Kudu maso gabas da APC ta yi rashin adalci ne ga yankinsu.

Idan aka zo zaben gwamna, Agbaso yana tare da APC, amma a zaben shugabancin kasa, tsohon mataimakin gwamnan zai tsallaka zuwa jam’iyyar adawa.

Da yake magana, Agbaso ya yabi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na sa hannu a sabuwar dokar zabe, yana cewa 2023 dama ce da za a kawo sauyi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu
Gwamnan Imo tare da Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Agbaso ya na tare da Obi a sama

“Zan goyi bayan APC a zaben jiha, amma a takarar shugaban kasa, zan marawa Peter Obi baya ne.”
“Domin kuwa idan har zai iya tabuka abin kirki, ya motsa kasa, kuma ya samu alfarmar mutane sosai, ya kamata a ba shi karfin gwiwa a zaben (2023).”

Rahoton ya ce Agbaso wanda ya taba rike Kwamishinan ayyuka a Imo yana tuhumar jam’iyyarsa ta APC da maida ‘Yan kudu maso gabas saniyan ware.

Kara karanta wannan

Kungiyar Ma’aikata da ‘Yan kasuwan Najeriya sun tsaida ‘Dan takaran 2023 da za su zaba

A cewarsa, a lokacin zaben ‘dan takarar shugaban kasa, sun yi tunanin za a ba su tikiti. A karshe Bola Tinubu daga yankin Arewa maso yamma ne ya yi nasara.

Cif Agbaso ya ce a wurinsa ba adalci ba ne APC ta tsaida Bayarabe a matsayin ‘dan takara a 2023.

Amma wannan mataki da tsohon mataimakin gwamnan ya dauka tamkar yi wa jam’iyya zagon-kasa ne. Ba mu san ta yadda APC za ta duba lamarin na sa ba.

Fayose sun juyawa Atiku baya

Kun samu rahoto cewa Ayo Peter Fayose yana nan kan bakarsa, yace har abada ba za su goyawa Atiku Abubakar baya ba domin bai dace mulki ya koma Arewa ba.

Tsohon gwamnan ya zargi ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar da cin amanar Nyesom Wike bayan yi masa alkawarin zama 'dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng