2023: Sowore ya zakulo 'Dan Kano da zai ‘taimaka’ masa wajen doke Kwankwaso a Kano
- Omoyele Sowore ya fitar da wanda zai zama masa ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a AAC
- Dan takarar shugaban Najeriyan ya dauko mutumin Kano da nufin samun kuri’u daga jihar a 2023
- AAC ta na sa ran Haruna Garba Magashi zai taimaka mata wajen yin galaba a kan APC da NNPP
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - ‘Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar African Action Congress, Omoyele Sowore, ya tsaida wanda zai zama abokin takararsa a zaben 2023.
Punch ta fitar da rahoto a yammacin Alhamis, 30 ga watan Yuni 2022, da ya ce Sowore ya zabi Haruna Garba Magashi esq. a matsayin mataimakinsa.
Bayan daukar lokaci ana jiran a ji wanda zai zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar hamayyar ta ADC, Sowore ya bada sanarwa.
‘Dan siyasar ya fito da abokin takararsa ne daga jihar Kano a yankin Arewa maso yammacin kasar. Sowore ya wallafa bidiyon taron a Facebook.
Haruna Garba Magashi wanda Lauya ne, shi ne zai rike tutar jam’iyyar ta ADC tare da Sowore mai shekara 43 wanda yake neman zama shugaban kasa.
Wani rahoton da muka samu ya ce Sowore ya sanar da Duniya cewa Haruna Magashi zai rike masa tikiti, kuma shi yake sa ran ya kawo masu kuri'u.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin Omoyele Sowore
“Mu na sa ran mu doke APC a nan domin Gwamnan ya jagwalgwala abubuwa, mun san za mu doke PDP, domin yanzu haka jam’iyyar na cikin rikici.”
“Ba mu bukatar mu yi magana a game da Labour Party, domin a Kano ba a san da zamanta ba.”
“Mun san za mu doke Kwankwaso da jam’iyyar sa ta NNPP a jihar Kano, domin kuwa mun samo wanda (Haruna Garba Magashi) shi daga jihar ya fito.”
- Omoyele Sowore
Ko 2023 zai bambanta da 2019?
A zaben 2019, Omoyele Sowore ya samu kuri'u 33,953 ne a fadin Najeriya. Wannan karo ya na tunanin jam'iyyar hamayyar ta AAC za ta tabuka abin kwarai.
Tuni AAC ta aikawa INEC sunan Magashi a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa. Sai dai Legit.ng Hausa ba ta da labarin tarihin Magashi a siyasa.
Peter Obi ya samu kwarin gwiwa
A zaben shugaban kasa da za ayi a farkon 2023, an ji labari shugabannin kungiyar TUC da NLC sun hadu kan ‘dan takaran Labor Party, Peter Obi za su ba kuri’a.
Ayuba Wabba ya umarci ‘yan kwadagon kasar nan su zabi Obi, wannan shi ne kiran da Quadri Olaleye ya yi wa kungiyar ‘yan kasuwa wajen wani taro da suka yi.
Asali: Legit.ng