Buhari ya saki muhimmin sako game da zaben 2023, ya bayyana abun da zai yi

Buhari ya saki muhimmin sako game da zaben 2023, ya bayyana abun da zai yi

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai ba hukumar INEC cikakken yanci don gudanar da babban zaben 2023 cikin gaskiya da amana
  • Buhari ya bayar da wannan tabbacin ne a cikin wani sako da ya saki daga Lisbon, kasar Potugal, a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni
  • Ya kuma kara tabbatar da cewar gwamnatinsa ba za ta yi katsalandan a gudanarwar zaben ba duk rintsi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Portugal – Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar zai kasance a tsaka-tsaki a babban zaben 2023 mai zuwa .

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, yayin da yake jawabi ga yan Najeriya mazauna Portugal a Lisbon, babbar birnin kasar.

Ya kuma bayyana cewa zai ba hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) cikakken yancin gudanar da zabe na gaskiya da amana.

Kara karanta wannan

Za mu durkusa a gaban Wike idan hakan zai sa ya ci gaba da zama a PDP, in ji Walid Jibrin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Buhari ya saki muhimmin sako game da zaben 2023, ya bayyana abun da zai yi Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa tunda yanzu an kammala zaben fidda gwani na yan takarar shugaban kasa a fadin jam’iyyun siyasa, yanzu hankali gaba daya ya karkata ne kan zabukan 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Muna duba zuwa ga mika mulki ga gwamnati na gaba cikin nasara. Kamar yadda na fadi a baya, gwamnatinmu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen aikata abubuwan da suka dace da jin dadin yan Najeriya na gida da waje ba.”

Da yake misali da zabukan gwamnan Ekiti da Anambra, shugaban kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa ta tabbatar da cewa ba za ta yarda da katsalandar a zabuka ba sannan kuma cewa a bari yan Najeriya su zabi jam’iyyu da yan takarar da suke so, PM News ta rahoto.

Shugaban kasar ya kuma yi amfani da wannan damar wajen gargadi kan amfani da shafukan soshiyal midiya don cin zarafi da tunzura jama’a daga nesa, yana mai umurtan yan kasar mazauna waje da su dunga bunkasa hadin kan Najeriya.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

Zaben 2023: APC za ta kaddamar da tashar yanar gizo da za ta sa a dama da matasa a siyasa

A wani labari na daban, Jam’iyyar APC mai mulki ba shirya wasa ba, domin ta shirya kaddamar da shafin yanar gizo domin hada kan matasa kafin zaben shugaban kasa na 2023.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya bayyana shirin ne a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni a Abuja.

Mista Israel ya bayyana cewa sabon shirin an yi shi ne domin tabbatar da damawa da matasa a harkokin siyasar jam'iyyar. Ya ce dandali ne da ake son amfani dashi wajen jawo hankalin matasa zuwa jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng