Zaben 2023: APC za ta kaddamar da tashar yanar gizo da za ta sa a dama da matasa a siyasa

Zaben 2023: APC za ta kaddamar da tashar yanar gizo da za ta sa a dama da matasa a siyasa

  • Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, jam'iyyar APC mai mulki ta ci gaba da himma a shirye-shiryen ci gaba da rike matsayinta na mulkin Najeriya
  • Kungiyar matasan jam’iyyar APC na daf da kaddamar da wata kafar yanar gizo ta musamman da nufin fara rijista da kuma sabunta sunayen matasan jam'iyyar
  • Kodinetan matasa na jam'iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya ce shirin zai ba da damar shiga siyasa da kuma damawa da matasa

Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ba shirya wasa ba, domin ta shirya kaddamar da shafin yanar gizo domin hada kan matasa kafin zaben shugaban kasa na 2023.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya bayyana shirin ne a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni a Abuja.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Buhari ya gaza bibiyar kalamansa da aiki, 'Dan majalisar wakilai na APC

APC za ta kaddamar da tashar yanar gizo don rajistar matasa
Zaben 2023: APC za ta kaddamar da hanyar rajistan jam'iyya ta yanar gizo | Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

Mista Israel ya bayyana cewa sabon shirin an yi shi ne domin tabbatar da damawa da matasa a harkokin siyasar jam'iyyar. Ya ce dandali ne da ake son amfani dashi wajen jawo hankalin matasa zuwa jam’iyyar.

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Za mu hada hannu da dukkan manyan mashawarta na musamman (SSA) da masu ba da shawara na musamman kan matasa a fadin jihohi 36 na kasar nan, ciki har da babban birnin tarayya (FCT).
“Za mu tabbatar da cewa suna da tasiri ga matasa a jihohinsu daban-daban; za mu hada kai da gwamnoninmu don tabbatar da cewa suna samar da romon dimokuradiyya a jihohinsu.”

Yayin kaddamar da kwamitin na musamman na reshen matasan jam’iyyar APC na kasa kan gyara da rajista ta matasan APC, Israel ya bayyana cewa za a gudanar da atisayen ne daga ranar Juma’a 1 ga watan Yuli zuwa Lahadi 31 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar matasan APC sun dage, sun ce Zulum ne ya kamata ya yi takara da Tinubu

Ya lura da cewa atisayen na nuni da tsagwaron daidaito, da tsari a cikin ayyuka da sauran abubuwan da suka shafi jam’iyyar. Israel ya kuma bayyana za a tabbatar da kayakkayawar kulawa da gudanarwa.

Tsarin rajistar ba zai zama da wahala ba, in ji Dayo Israel

Mista Israel ya kara da cewa hanyoyin da mutum zai iya yin rajista ba su da wata matsala domin ya hada da tantancewa da tace muhimman takardu don yin rajista da kuma musamman sake tantancewa.

Ya ce an zabo mambobin kwamitin ne domin tabbatar da samun nasara da kuma tsarin da ya dace ga matasa da kungiyoyin tallafa wa dalibai a cikin jam’iyyar, Pulse ta tattaro.

Mista Ben Duntoye, Shugaban kwamitin ya gode wa shugabannin jam’iyyar bisa damar da suka ba su na yi mata hidima, yana mai cewa babbar gata aka yi musu.

Ya ce wannan shiri abin a yaba ne kuma ya ba da tabbacin cewa kwamitin zai gudanar da aikin da aka dora masa a cikin wa’adin da aka ba shi.

Kara karanta wannan

Mu na tattaunawa da PDP da ‘Jam’iyyar kayan marmari’ inji ‘Danuwan Buhari, Hon. Fatihu

Ya kuma ce mambobin kwamitin sun cancanta kuma ba za su ba jam’iyyar da Najeriya da matasa kunya ba.

Zaben fidda gwanin APC: Yadda deliget 17 suka mayar min da kudi na, inji Sanata

A wani labarin, dan majalisa mai wakiltar yankin Kwara ta tsakiya, Sanata Ibrahim Oloriegbe, ya ce wasu deliget da ya ba da kudade a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar sun mayar masa da abin sa.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Channels a shirin Sunrise Daily inda ya yi magana kan rikicin da ke cikin jam’iyyar mai mulki.

Sanata Oloriegbe ya caccaki tsarin da aka bi wajen gudanar da zabukan fidda gwanin da aka yi a wasu jihohin, inda ya zargi gwamnoni da kakaba deliget ga magoya bayan jam’iyyar, rahoton Leadership.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.