Lauyoyi sun dumfari kotu, su na so a hana Atiku, Tinubu da Obi tsayawa takara a 2023
- An samu lauyoyin da suka yi karar ‘yan takaran jam’iyyun APC, PDP da LP a kotu kan zaben 2023
- Lauyoyin da suka je kotu sun ce ‘yan takaran duk sun saba doka da tsarin mulki a zaben tsaida gwani
- Masu karar su na ikirarin ya kamata a fitar da ‘yan takarar mataimakin shugaban kasa kafin yanzu
Abuja - Wasu lauyoyi sun roki kotu ta dakatar da manyan ‘yan takaran da ake da su, daga shiga zaben shugaban kasa da hukumar INEC za ta shirya a 2023.
Daily Trust ta ce wadannan lauyoyi uku sun nemi kotun tarayya da ke zama a garin Abuja ta rusa neman takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a jam’iyyar APC.
Har ila yau lauyoyin su na so a hana ‘dan takaran jam’iyyar adawa ta PDP watau Atiku Abubakar da kuma Peter Obi tsayawa neman shugabanci a zaben 2023.
Peter Obi shi ne wanda zai yi wa jam’iyyar nan ta Labor Party takara a zaben shekara mai zuwa.
Lauyoyin da suka je kotu
Lauyoyin; Ataguba Aboje, Oghenovo Otemu, da Ahmed Yusuf su na ikirarin cewa wadannan jam’iyyun siyasa sun sabawa dokar zabe na 2022 da tsarin mulki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Inda APC, PDP da LP suka sabawa dokar kasar kuwa shi ne wajen zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasa da suka gudanar a watan nan na Yuni da ake ciki.
A cewar Ataguba Aboje, Oghenovo Otemu, da kuma Yusuf, ‘yan takaran ba su sanar da Duniya sunayen abokan takararsu kafin a fara zaben tsaida gwanin ba.
Jam'iyyu 3 sun saba doka
Hakan ta sa lauyoyin suka ce ya kamata Alkali ya hana Atiku Abubakar, Bola Tinubu da Peter Obi shiga zabe domin ba ta halaliyar hanya suka zama ‘yan takara ba.
Jaridar Tribune ta ce sauran wadanda ake kara a kotun tarayyan na Abuja sun hada da hukumar INEC, babban lauyan gwamnati, sai jam’iyyun APC, PDP da kuma LP.
A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1004/2022, lauyoyin sun bukaci kotu tayi amfani da sassa na 131, 141 da na 142 domin yanke hukunci a wannan shari’a da ke gabanta.
Haka zalika rahoton ya ce Lauyoyin su na so Alkali ya fede abin da sassa na 29, 32, 84 da 152 na dokar zabe ta ce a game da ‘dan takarar mataimakin shugaba kasa.
Har yanzu ba a sa ranar da za a fara sauraron wannan shari’a a gaban kotun mai zama a Abuja.
An kai Tinubu kotu
Kwanakin baya an ji labari lauyan da ya shigarwa Action Alliance da kara a gaban Alkali ya na tuhumar Bola Tibubu da zargin yi wa hukumar INEC karya a 1999.
Barista Ukpai Ukairo yana zargin APC da ‘dan takaran jam’iyyar a 2023 da saba doka ta hanyar yin karyar ya yi karatu, alhali bai halarci makarantun da yake ikirari ba.
Asali: Legit.ng