Jam’iyyar AA ta shigar da karar Bola Tinubu, ana so a hana APC takarar Shugaban kasa

Jam’iyyar AA ta shigar da karar Bola Tinubu, ana so a hana APC takarar Shugaban kasa

  • Action Alliance (AA) za ta yi shari’a a kotu da jam’iyyar APC da ‘dan takararta watau Bola Tinubu
  • Lauyan Action Alliance yace Tinubu ya yi amfani da takardun bogi, don haka bai dace da takara ba
  • Idan jam’iyyar hamayyar ta samu yadda ta ke so, za a hana APC da ‘dan takararta shiga zaben 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Action Alliance (AA) ta roki babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja, ta umarci hukumar INEC ta cire jam’iyyar APC daga yin takaran 2023.

Daily Trust ta ce Action Alliance ta na kuma so a haramtawa ‘dan takarar APC, Asiwaju Bola Tinubu neman kujerar shugaban kasa saboda zargin badakala.

Ana zargin cewa Bola Tinubu bai da takardar shaidar zuwa makaranta, zargin da an musanya.

A wannan kara da aka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/954/2022, lauyan AA sun fadawa Alkali cewa APC da ‘dan takararta ba su dace su shiga zaben badi ba.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa APC ta hana ni damar komawa Majalisa – Sanata ya fayyace komai

Lauyoyin da suka kai kara sun ce Bola Tinubu ya yi wa Duniya karya da takardun jabu a 1999. A cewarsu, Tinubu ya fake da shaidar karatun da bai mallaka ba.

Tinubu ya yi karatun boko?

‘Dan takaran shugaban kasar na APC ya na ikirarin ya halarci makarantun St. Paul’s Aroloya Children’s Home School da Government College da su ke Ibadan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bola Tinubu
Bola Tinubu tare da Oba na Legas Hoto: officialasiwajubat
Asali: Facebook

Bugu da kari, tsohon gwamnan na jihar Legas ya ce ya yi karatu a Richard Daley College da jami’ar jihar Chicago, duk a yankin Illinois a kasar Amurka.

A wata takarda da Kalu Agu ya bada shaida, ya ce wanda ake tuhuma ya san bai halarci makarantun nan ba, amma ya yi wa INEC karya a fam dinsa.

Lauya ya kafa hujja

Ukpai Ukairo wanda ya tsayawa AA ya ce idan aka duba sashe na 24 da na 224 na kundin tsarin mulki, bai dace mara gaskiya ya dare kujerar shugaban kasa ba.

Kara karanta wannan

Takardun makarantar da Atiku, Tinubu, Kwankwaso da Obi suka gabatarwa hukumar INEC

Jaridar New Telegraph ta ce har zuwa yanzu, ba a sa lokacin da za a saurari wannan kara ba. Idan an zabi ranar da za a soma shari’ar, Tinubu zai san makomarsa.

Masari bai da takardu

Dazu kun ji cewa Shi ma abokin takarar Bola Tinubu watau Kabiru Ibrahim Masari ya tabbatar da cewa takardun shaidar duk karatun da ya yi sun bace a garin Abuja.

Masari ya sanar da ‘yan sanda game da batun bacewar satifiket din na sa, har ya rubuta takardar rantsuwa domin ya iya wanke kansa ko da an tsinci takardun na sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel