Hadimin gwamnan APC ya yi murabus daga muƙaminsa, ya nemi a ba shi miliyan N77.2m

Hadimin gwamnan APC ya yi murabus daga muƙaminsa, ya nemi a ba shi miliyan N77.2m

  • Wani rikici ya ɓarke a gwamnatin jihar Imo yayin da mai ba da shawari na musamman kan harkokin siyasa ga gwamna ya aje aikinsa
  • Batos Nwadike, ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bisa tilas saboda an watsar da ofishinsa ba'a tura masa kasafin kuɗi
  • Gwamnan ya ƙarɓi takardan tare da amincewa da murabus ɗin, kana ya masa fatan Alkairi a siyasarsa ta gaba

Imo - Wani rikici ya kunno kai a gwamnatin jihar Imo biyo bayan murabus ɗin mashawarci na musamman kan harkokin siyasa ga gwamna Hope Uzodinma, Batos Nwadike.

Daily Trust ta ruwaito cewa bayan mika takardan murabus ɗinsa, Nwadike, ya nemi a ba shi zunzurutun kuɗi Miliyan N77.2, wanda a cewarsa ya kashe su yayin da yake Ofis.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yayin da APC ke kokarin ɗinke barakar majalisa, Wani Sanata ya fice daga jam'iyyar

Nwadike na ɗaya daga cikin mambobin gwamnatin gwamna Uzodinma masu matuƙar muhinmanci da amfani.

Gwamna Uzodinma da Hadiminsa mai murabus.
Hadimin gwamnan APC ya yi murabus daga muƙaminsa, ya nemi a ba shi miliyan N77.2m Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Amma a takardar da ya aike wa gwamnan mai ɗauke da kwanan watan 22 ga watan Yuni, 2022, ya ce tilas akai masa ya aje aiki saboda an watsar da ofishinsa kuma ba'a tura masa kasafin kuɗi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, tsawon watanni 28 da ya kwashe a Ofis, ya kashe kuɗaɗen da suka kai miliyan N77.2m kan albashin ma'aikatansa da kuma gyara wuraren da ke ƙarƙashinsa.

A takardar ya ce:

"Ina mai alfahari da dana sanin rubuta cewa na yi murabus daga muƙamin mai ba da shawara kan harkokin siyasa."

Ya ce duk da sadaukarwan da ya yi wa gwamnatin, amma aka watsar da shi daga kowane harkoki, inda ya ƙara da cewa:

"An bar ni cikin duhu kuma aka hana ni shiga duk wasu lamurran tafiyar da mulki duk da rawar da na taka har zuwa wannan matsayin tun daga 2001 zuwa 2020."

Kara karanta wannan

Labari Cikin Hotuna: Sanata Kwankwaso ya kai ziyara Patakwal, ya sa Labule da gwamna Wike

Wane mataki gwamnan ya ɗauka?

Kwamishinan yaɗa labarai da dabaru, Declan Emelumba, ya bayyana cewa gwamnati ta karbi takardar murabus din Nwadike, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Da yake jawabi ga wakilin jaridar, Kwamishinan ya ce:

"Mai girma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya amince da murabus ɗinsa, ya gode masa bisa gudummuwar da ya bayar tare da masa fata nagari a duk abinda ya sa a gaba.

A wani labarin kuma Sabon rikici ya kunno kai a Yobe ta arewa, wani ɗan takara ya maka Machina a Kotu

Rikici kan tikitin takarar Sanata mai wakiltar Yobe ta arewa ya buɗe sabon babi, yayin da wani ɗan takara, Abubakar Abubakar Jinjiri, ya ƙalubalanci nasarar Bashir Sheriff Machina, a Kotu.

Machina, wanda ya samu kuri'u 289 da zaɓen fidda gwani, yanzu haka yana fafatawa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan kan tikitin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel