Tsohon ɗan takarar gwamna, Hadimin gwamna jigon PDP sun sauya sheƙa zuwa NNPP
- Yayin da yan siyasa ke cigaba da tashi daga nan zuwa can, jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta yi babban kamu a jihar Kwara
- Tsohon ɗan takarar gwamna da ɗan uwan tsohon shugaban majalisar Dattawa sun sauya sheka daga jam'iyyun su zuwa NNPP
- Shugaban jam'iyyar NNPP ta jihar Kwara ya bayyana wanda suka zaɓa a matsayin ɗan takarar gwamna
Kwara - Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarkashin inuwar jam'iyyar SDP a jihar Kwara, Farfesa Shuaib Abdulraheem Oba, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai kayan marmari wato NNPP.
Daily Trust ta rahoto cewa Oba na ɗaya daga cikin waɗan da suka ja ragamar tafiyar 'Otoge' ta jam'iyyar APC yayin babban zaɓen 2019 a jihar Kwara.
Hakanan kuma, tsohon hadimin gwamnan Kwara kan harkokin cigaba SDG, Alhaji Ope Saraki, ya bi sahu, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa NNPP Mai kayan daɗi.
Ope Saraki, ɗan uwa ne ga tsohon gwamnan Kwara kuma tsohon shugaban majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake jawabi a wurin taron da aka shirya don tarban su, Farfesa Oba ya bayyana cewa ya shiga jam'iyyar ne saboda gaskiyarta wanda a cewarsa aka rasa a sauran jam'iyyun siyasa.
Ya ce:
"A tattare da Mallam Rabiu Musa Kwankwaso, ɗan takarar mu na shugaban ƙasa, muna da mutum mai gaskiya wanda ya shirya sadaukarwa don cigaban ƙasa. NNPP jam'iyya ce da zata tabbatar mana da sabuwar Kwara da Najeriya wacce muke mafarki."
Meyasa ɗan uwan Saraki ya bar PDP?
A na shi jawabin, ɗan uwan Bukola Saraki, wato Ope Saraki, ya ce haɗakarsa da jam'iyyar NNPP ba wani abun mamaki bane.
Da aka tambaye shi meyasa ya bar PDP da ɗan uwansa, Ope ya amsa da cewa:
"Ni ɗan Najeriya ne ina da yanci kuma zan iya yanke shawari da aiki da kowace jam'iyya don cigaban mutane. A tare da Kwankwaso, ɗan takarar mu na shugaban ƙasa, muna ganin sabuwar Najeriya."
Wa NNPP ta tsayar takarar gwamnan Kwara?
Shugaban NNPP na jihar Kwara, AbdulRazaq Abdulsalam, ya sanar da cewa jam'iyya ta zaɓi Oba a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar a babban zaɓen 2023.
"Mun zaɓi Farfesa Shuaib Oba a matsayin ɗan takarar mu na gwamnan jihar Kwara a zaɓen 2023. Zai halarci taron ƴan takarar gwamna na NNPP a Abuja ranar Talata."
A wani labarin kuma Hadimin gwamnan APC ya yi murabus daga muƙaminsa, ya nemi a ba shi miliyan N77.2m
Wani rikici ya ɓarke a gwamnatin jihar Imo yayin da mai ba da shawari na musamman kan harkokin siyasa ga gwamna ya aje aikinsa.
Batos Nwadike, ya bayyana cew a ya ɗauki matakin ne bisa tilas saboda an watsar da ofishinsa ba'a tura masa kasafin kuɗi.
Asali: Legit.ng