Labari da Hotuna: Kwankwaso ya ziyarci gwamna Wike a Patakwal

Labari da Hotuna: Kwankwaso ya ziyarci gwamna Wike a Patakwal

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai ziyara ga gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a gidansa da ke Patakwal ranar Jumu'a
  • Yayin ziyarar, Kwankwaso, ɗan takarar shugaban kasa na NNPP ya sa labule da Wike, ba'a san me suka tattauna ba
  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya samu halartar tattaunawar, wacce ake ganin tana da alaƙa da zaɓen 2023

Rivers - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai kayan marmari wato NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai ziyara ga gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike, ranar Jumu'a a Patakwal.

Yayin da babu wani cikakken bayani kan dalilin ziyarar da abin da aka tattauna, ana ganin taron na su ba zai rasa alaƙa da babban zaɓen 2023 ba.

Wike da Kwankwaso.
Labari da Hotuna: Kwankwaso ya ziyarci gwamna Wike a Patakwal Hoto: Saifullahi Hassan/facebook
Asali: UGC

Hadimin tsoho gwamnan Kano kan harkokin midiya, Honorabul Saifullahi Hassan, ya sanya Hotunan Kwankwaso tare da Wike a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Yau Kwankwaso zai yi zama na musamman da Nyesom Wike a kan shirin zaben 2023

Haka nan kuma wani babban jigon siyasa da ya halarci ganawar a yau shi ne tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran jiga-jigan siyasa da suka ziyarci gwamna Wike kafin zuwan Kwankwaso sun haɗa da ɗan takarar shugabban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, gwamna Bala Muhammed na Bauchi da sauran su.

Hotunan Kwankwaso yayin ziyara ga Wike

Gwamna Wike da Kwankwaso.
Labari da Hotuna: Kwankwaso ya ziyarci gwamna Wike a Patakwal Hoto: Marshal Obuzor/facebook
Asali: Facebook

Wike da Kwankwaso.
Labari da Hotuna: Kwankwaso ya ziyarci gwamna Wike a Patakwal Hoto: Hon Saifullahi Hassan/facebook
Asali: Facebook

Sanata Kwankwaso da gwamna Wike.
Labari da Hotuna: Kwankwaso ya ziyarci gwamna Wike a Patakwal Hoto: Hon saifullahi hassan/facebook
Asali: Facebook

Ziyarar Kwankwaso Patakwal.
Labari da Hotuna: Kwankwaso ya ziyarci gwamna Wike a Patakwal Hoto: Hon Saifullahi Hassan/facebook
Asali: Facebook

A wani labarin kuma Sabon rikici ya kunno kai a Yobe ta arewa, wani ɗan takara ya maka Machina a Kotu

Rikici kan tikitin takarar Sanata mai wakiltar Yobe ta arewa ya buɗe sabon babi, yayin da wani ɗan takara, Abubakar Abubakar Jinjiri, ya ƙalubalanci nasarar Bashir Sheriff Machina, a Kotu.

Machina, wanda ya samu kuri'u 289 da zaɓen fidda gwani, yanzu haka yana fafatawa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan kan tikitin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sanatacin PDP sun sa labule da gwamna Wike bayan tafiyar Orubebe

Asali: Legit.ng

Online view pixel