Ba zan bar harkar siyasa ba, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ga magoya bayansa

Ba zan bar harkar siyasa ba, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ga magoya bayansa

  • Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayar da tabbacin ci gaba da kasance a cikin harkokin siyasar kasar nan
  • Osinbajo wanda ya sha kaye a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya ce zai ci gaba da fafutukarsa na son ganin kasar Najeriya ta inganta
  • Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa tare da kungiyar magoya bayansa da ke zaune a kasar waje

Abuja - Bayan rashin cikar burinsa na son gadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce zai ci gaba da kasancewa a cikin harkar siyasa.

Osinbajo ya kuma bayyana cewa zai ci gaba da fafutukar son ganin Najeriya ta inganta kamar yadda Arise News ta rahoto.

Yemi Osinbajo
Ba zan bar harkar siyasa ba, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ga magoya bayansa Hoto: Professor Yemi Osinbajo
Asali: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga wakilan kungiyar magoya bayansa na PYO a kasar waje a wani taro da suka yi ta yanar gizo.

Kara karanta wannan

2023: A Karshe, Igbo Sun Bayyana Wanda Za Su Zaba Tsakanin Tsakanin Tinubu, Atiku Da Obi

Hakan na kuma kunshe ne a cikin Wata sanarwa daga hadimin labaransa, Mista Laolu Akande.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Thisday ta nakalto Osinbajo yana cewa:

“Ina da niyan ci gaba da kasancewa a harkar siyasar kasarmu, saboda na yarda cewa idan Allah ya bamu wannan damar, Chanji zai zo kuma za mu kawo sauyi na gaske.
“Ya zama dole mu ci gaba da turawa. Idan muka gaji sannan muka ce bari muga yadda abun zai kasance, za kara komawa baya fiye da yadda muka fara.”

A lokacin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta gudanar da taronta na musamman don zabar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar na zaben 2023 a Eagles Square Abuja, Osinbajo ne ya zo na uku.

Ya biyo bayan tsohon gwamnan jihar Lagas, Bola Tinubu da tsohon ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Akwai wasu miyagun mutane da ke shirin sanya Najeriya cikin garari

2023: Osinbajo na fuskantar matsin lamba don sake shiga tseren shugaban kasa, an nemi ya hade da Kwankwaso

A wani labarin kuma, mun ji cewa ana kulla-kulla don hada kawance tsakanin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da sansanin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a kokarin ganin ya dawo tseren shugaban kasa na 2023.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa majiyoyi a sansanonin biyu sun dage cewa akwai shawarwari masu karfi da ke gudana dangane da yiwuwar samun tikitin Osinbajo/Kwankwaso a karkashin inuwar jam’iyyar NNPP.

A cewar majiyoyin, wasu hadiman mataimakin shugaban kasar tare da hadin gwiwar wasu manyan yan siyasar arewa ne suke jagorantar wannan yunkurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng