2023: A Karshe, Igbo Sun Bayyana Wanda Za Su Zaba Tsakanin Tsakanin Tinubu, Atiku Da Obi

2023: A Karshe, Igbo Sun Bayyana Wanda Za Su Zaba Tsakanin Tsakanin Tinubu, Atiku Da Obi

  • Mutanen yankin kudu maso gabas sun bayyana wanda za su zaba a matsayin shugaban kasa a zaben 2023
  • Kungiyar dattawan kungiyar tuntuba ta Igbo mai suna Ime-Obi Ohanaeze Ndigbo ne ta bada sanarwar
  • A cewarsu, kamata ya yi shugabancin kasar ya tafi sashin kudu maso gabas tunda ba su taba fitar da shugaban kasa ba

An soki jam'iyyar APC mai mulki da babban jam'iyyar hamayya ta PDP saboda kin bawa yankin kudu maso gabas shugabancin kasa.

Wannan shine matsayin kungiyar tuntuba ta dattawan Igbo mai suna Ime-Obi Ohanaeze Ndigbo.

Muhammadu Buhari
2023: A Karshe, Igbo Sun Bayyana Wanda Za Su Zaba Tsakanin Tsakanin Tinubu, Atiku Da Obi
Asali: Depositphotos

Punch ta rahoto cewa dattawan sun soki daligets din igbo wadanda suka ki zaben yan takara daga yankin kudu maso gabas a zaben fidda gwani na takarar zaben shugaban kasa na 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Buhari Ya Sake Jaddada Cewa Sai An Ladabtar Da 'Yan Ta'adda, Ya kwatantasu da Ragwaye

Kungiyar ta kuma bayyana su a matsayin 'maciya amana marasa kunya'.

Kungiyar ta IECF a cikin sanarwar da ta fitar a Abuja ta bakin sakatarenta Farfesa Charles Nwekeaku ta ce:

"Wannan ba zai sake faruwa ba duba da cewa dattawan Igbo za su bada jagoranci da zai karfafa shugabancin kasa. Wadanda suka ci amanar mu za su yi ritaya daga siyasa don babu wanda zai sake zabensu su wakilci kudu maso gabas kuma.
"Mun saka ido, mun kuma damu ganin yadda aka mayar da siyasar ta kudi a zaben cikin gida na shugaban kasa da aka yi a baya-bayan nan inda wanda ya fi kudi ne ya yi nasara.
"Abin da ya fi damunmu, shine yadda manyan jam'iyyun siyasa, APC da PDP suka ki mayar da mulki yankin kudu kamar yadda ya ke a sashi na 14 (3) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya da jam'iyyun siyasa daban-daban saboda adalci, dai-daito, zaman lafiya a kasar.

Kara karanta wannan

Peter Obi danmu ne amma Atiku za mu yi a kudu maso gabas – Ekweremadu

"Bugu da kari, girman kai irin na shugabannin PDP an canja dokar ya nuna ba su damu da adalci, dai-daito ba da aka zo lokacin kudu maso gabas ta fitar da shugaban kasa.
"Abin tada hankali kuma shine yadda wasu yayanmu na Igbo marasa kishin yankin da suka hada kai da wadanda ba su nufin mu da alheri don hana yan yankin mu samun takara ta hanyar kin basu kuri'u.
"Sun yi aiki sun zabi dalla a madadin yan takara daga yankin kudu maso gabas suka ki bin umurnin kungiyar gwamnonin kudu, kungiyar kudu da tsakiya, Afenifere, Pan Niger Delta Forum, Igbo Consultative Forum, Ohaneze Global da wasu masu ruwa da tsaki da suka goyi bayan a mayar da mulki kudu, kuma kudu maso gabas.
"Banda Jihar Ebonyi, sauran daliget daga Jihohin Anambra, Abia, Enugu da Imo da masu daukan nauyinsu za su fada wa Ndi Igbo wadanda suka sayarwa kuri'unsu kuma nawa a madadin damar da yankin za ta samu na fitar da shugaban kasa a 2023."

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Peter Obi ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a Port Harcourt

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.

Asali: Legit.ng

Online view pixel